Bode George na neman takarar Shugabancin PDP

Bode George na neman takarar Shugabancin PDP

- Mr. Bode George na neman takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP

- George ya sha alwashin tika APC da kasa idan ya ci ma burin sa

- Sai dai Bode George zai gamu da cikas wajen wannan yunkuri

Mun ji labari daga Jaridar Daily Trust cewa Bode George ya nemi fitowa takarar Shugaban Jam’iyyar PDP mai adawa.

Bode George na neman takarar Shugabancin PDP

Bode George ya sha alwashin ba APC kashi a 2019

Mr. Bode George wanda shi ne tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar ta PDP yana neman takarar Shugabancin Jam’iyyar a zabe mai zuwa. George ya kaddamar da niyyar na sa ne a wani dakin taro a Legas inda manyan ‘Yan Jam’iyyar da dama su ka halarta.

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP ta hurowa Shugaba Buhari wuta

Bode George ya yabawa irin kokarin Shugaban Jam’iyyar na rikon kwarya watau Ahmad Muhammad Makarfi da mutanen sa da irin aikin su wajen jan ragamar Jam’iyyar. George yace idan Jam’iyar ta karbi mulki za a gyara tattalin arzikin kasar nan.

Kamar yadda mu ka samu labari dai kwanaki ana kuma kokarin kakaba wani tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar a lokacin Ahmad Adamu Mu’azu ne matsayin Shugaban Jam’iyyar da zarar Ahmad Makarfi ya kammala wa’adin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel