Ayyuka 25 da Gwamnatin Shugaba Buhari za tayi da kudin ‘sukuk’

Ayyuka 25 da Gwamnatin Shugaba Buhari za tayi da kudin ‘sukuk’

- Mun kawo jerin wasu ayyuka 25 da Gwamnatin nan za tayi

- Za a gina tituna dabam-dabam a kowane bangare na fadin kasar

- Yankin Kudu-maso-kudu ne su ka fi samun kaso mafi tsoka

Dazu mu ke samun labari irin ayyukan titunan da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zai gina a barin kasar nan.

Ayyuka 25 da Gwamnatin Shugaba Buhari za tayi da kudin ‘sukuk’

Wata mummunar hanya a Najeriya

Za a dai yi wannan aiki ne da kudin da aka samu na hannun jarin nan na ‘Sukuk’ a kowani yanki na Kasar da kudi kusan Naira Biliyan 17. Gwamnatin Tarayya za tayi aiki na sama da Naira Biliyan 100 cur!

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gana da Alkalin Alkalai

Yankin Arewa maso tsakiya za su samu tituna 5 daga ciki akwai titin Abuja zuwa Lokoja da kuma hanyar Suleja zuwa Minna.

Yankin Arewa maso gabas kuma za su ga an fadada hanyar Kano zuwa Maiduguri.

A Yankin Arewa maso yamma za a buda hanyar Kano zuwa Maiduguri da kuma ta Kano zuwa Kaduna da sauran su.

Yankin kudu maso gabas kuma za su ga canji a hanyar Onisha zuwa Enugu da kuma hanyar Enugu zuwa Fatakwal.

A kudu-maso-kudu za a gyara titin hanyar Garin Otuoke da kuma hanyar Lokoja zuwa Benin.

A bangaren Kudu-maso-yamma za a gyara titin Ilorin zuwa Ibadan da hanyar Garin Shagamu da sauran su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel