Andres Iniesta ya sanya hannu a kwantaragin zaman sa Barca har abada

Andres Iniesta ya sanya hannu a kwantaragin zaman sa Barca har abada

Shugaban tawagar yan kwallon kungiyar Barcelona mai suna Andres Iniesta ya sanya hannu a wata yarjejeniya da ba kasafai ake yi ba inda dan wasan ya amince ya zauna a kungiyar har abada.

Yanzu haka dai dan wasan na kasar Spain ya yi wa kungiyar ta sa ta Barcelona wasannin da jumillar su ta kai 639 wanda hakan ne ya maida shi a matsayi na biyu cikin jerin yan wasan kungiyar da suka fi buga kwallo kuma ya zura kwallaye 55 kacal a raga.

Andres Iniesta ya sanya hannu a kwantaragin zaman sa Barca har abada

Andres Iniesta ya sanya hannu a kwantaragin zaman sa Barca har abada

KU KARANTA: Makarfi yayi magana game da takarar Fayose a 2019

NAIJ.com dai ta samu cewa dan wasan Andres Iniesta da yake buga tsakiyar fili ya je kungiyar ne kimanin shekaru 11 da suka wuce a shekarar 1996 kuma a lokacin yana da da shekara 12 a duniya.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa kungiyar ta Barcelona ta fara kakar wasannin bana da kafar dama inda ya zuwa yanzu bata samu tangarda ko sau daya ba da hakan ya bata damar zama a saman teburin gasar ta Laliga a matsayi na daya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel