Hattara: Cutar ‘Monkey Pox’ ta shigo Najeriya

Hattara: Cutar ‘Monkey Pox’ ta shigo Najeriya

- A halin yanzu an samu barkewar mugun cuta a Najeriya

- Cutar ‘Monkey Pox’ maras magani ta shigo kasar nan

- Har yanzu dai wannan cuta ba ta kashe kowa ba tukun

Kwanan nan mu ke jin labari cewa wata sabuwar cuta da ake kira da Turanci ‘Monkey Pox’ mara magani ta barke a Najeriya.

Hattara: Cutar ‘Monkey Pox’ ta shigo Najeriya

Kurajen cutar da ta shigo kasar nan

Yanzu haka wannan cutar da ke kama da kyanda ta barke a Kudancin kasar nan. Wannan cuta dai na sa kuraje su fesowa mutum a jiki. Wannan cutar ba ta da magani sai dai ayi ta kokarin rigakafi domin gudun daukar wannan cutar daga mutum ko dabbobin daji.

KU KARANTA: Shugaban Hukumar bada agaji ya kife har lahira

Wadannan kuraje na jawo zazzabi da laulayi da ciwon kai. Wadanda su kamu da wannan cuta sai su dage da shan maganin zazzabi. Sai kuma an bi a hankali kwarai da gaske wajen tsabta domin gudun kamuwa da wannan mugun cuta.

Dazu ku ka ji cewa nonon kwaron nan da ka sani kyankyaso na dauke da sinadaran gina jiki da dama wanda su ka hada da sukari da kuma sinadarin ‘fats’ mai sa kiba da kuma ‘furotin’ mai gina jiki kamar yadda wani bincike na Gidan CNN ya nuna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel