Zaben 2019: Shekarau ya sha alwashin fafatawa da shugaba Buhari

Zaben 2019: Shekarau ya sha alwashin fafatawa da shugaba Buhari

Yanzu haka dai labarin da ke iske mu yana nuna cewa tsohon Gwamnan jihar Kano kuma jigo a jam'iyyar PDP Malam Ibrahim Shekarau dai kawo yanzu ya kawo karshen kace-nacen da ake tayi na takarar sa a zabe mai zuwa na 2019.

Tsohon Gwamnan na Kano Malam Ibrahim Shekarau ya dai taba gwada sa’arsa a shekarar 2011 inda a jam’iyyar sa ta ANPP ya tsayar da shi takara ya kuma fafata da shugaba Muhammadu Buhari amma bai yi nasara ba.

Zaben 2019: Shekarau ya sha alwashin fafatawa da shugaba Buhari

Zaben 2019: Shekarau ya sha alwashin fafatawa da shugaba Buhari

KU KARANTA: Ma'aikatan man fetur na shirin shiga yajin aiki

NAIJ.com dai ta samu daga majiyar mu cewa tsohon ministan ilimin a gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ya fitar da wata takarda ne dauke da bayyana kudurin nasa ga wasu na kusa da shi da kuma abokan siyasar shi.

A cikin takardar dai mun samu cewa tsohon Gwamnan ya ce: “Kamar yadda ku ka sani tun tsawon lokaci bayan kammala zaɓen shekara ta 2015, ana ta kiraye-kiraye daga al’umma ana bukatar in fito takarar kujerar shugabancin kasa a zaben shekara ta 2019 to na amince."

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel