Jami'an kwastam sun kama motoci 3,665 daga 2015 zuwa yanzu

Jami'an kwastam sun kama motoci 3,665 daga 2015 zuwa yanzu

Shugaban hukumar dake sa ido tare kuma da hana fasa kwarin kayayyaki zuwa Najeriya Kanal Hameed Ali mai ritaya ya bayyana cewa hukumar da yake shugaban ta kwastam ta samu nasarar kama motocin alfarma kimanin 3,665 tin daga shekarar 2015 zuwa yanzu.

Haka nan kuma shugaban na hukumar ya bayyana cewa kudaden da suke sa ran motocin za suyi zai kai kimanin Naira biliyan 13 idan aka yi gwanjon su aka cirewa gwamnatin tarayya hakkin ta.

Jami'an kwastam sun kama motoci 3,665 daga 2015 zuwa yanzu

Jami'an kwastam sun kama motoci 3,665 daga 2015 zuwa yanzu

KU KARANTA: Za'a ba yan IBOB kyautar Naira 250,000

NAIJ.com ta samu dai cewa shugaban na kwastam yayi wannan bayanin ne a yayin wani babban taro da aka gayyace ya kuma gabatar da makala mai taken 'fasa kwauri da kuma tu'annatin da yake yi wa tattalin arzikin kasa.'

Haka ma dai mai karatu zai iya tuna cewa hukumar ta bayyanawa manema labarai wasu manyan haramtattun kayayykin da suka hada da shinkafa, motoci, man olga da dai sauran su da suka kama daga watan Agusta zuwa wannan watan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taro a kan dumaman yanayi

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taro a kan dumaman yanayi

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taro a kan dumaman yanayi
NAIJ.com
Mailfire view pixel