Kyandar birai: Gwamnatin tarayya ta gargadi yan Najeriya game da cin naman biri

Kyandar birai: Gwamnatin tarayya ta gargadi yan Najeriya game da cin naman biri

Mahukunta a Najeriya musamman ma na fannin lafiya sun gargadi illahirin al'ummar kasar da su guji cin naman biri da sauran naman daji biyo bayan barkewar annobar cutar kyandar birai da aka samu a jihar Bayelsa da ke a kudancin kasar a karshen satin nan.

Alkaluma da dama dai daga mutane da yawa sun tabbatar da cewa ya zuwa yanzu a kalla mutane 10 ne aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar inda kuma tuni a ka kebe su don gudun kada ta yadu zuwa wasu.

Kyandar birai: Gwamnatin tarayya ta gargadi yan Najeriya game da cin naman biri

Kyandar birai: Gwamnatin tarayya ta gargadi yan Najeriya game da cin naman biri

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya kusa kamuwa da hawan jini - Amaechi

NAIJ.com dai ta samu cewa cikin wata sanarwa da ministan lafiyar kasar Farfesa Isaac Adewole ya fitar, ya bayyana cewa ana cigaba da bincike kan ainihin musabbabin dalilin da ya jawo cutar tun a karon fari. Haka ma dai binciken mu ya tabbatar mana cewa ita dai wannan cutar ana samun ta ne a jikin dabbobin daji irin su birrai da bera da kurege da kuma barewa.

Haka kuma dai majiyar mu ta ruwaito cewa akwai Likita 1 a cikin mutune 10 da aka kebe.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel