Mai dokar bacci: Maigadi ya tafka sata ranar da aka dauke shi aiki

Mai dokar bacci: Maigadi ya tafka sata ranar da aka dauke shi aiki

- Ya sace wata mota kirar Hyundai da darajarta ya kai naira miliyan 5

- An kama maigadin a yankin Iyana Oworo a hanyar sa ta zuwa jihar Benuwe bayan da motar da ya sato ta mutu yana cikin tafiya

- Mai laifin ya amsa laifin sa, sannan ya bayyana cewar ya saci motar ne domin ya je jihar Benuwe yake haya da ita ko kuma ya sayar domin samun jarin fara yin sana'a

Wani maigadi, Joseph Aba, karkashin wani kamfanin samar da tsaro mai zaman kan sa, Halogen Security Services Limited, dake Legas, ya sace wata mota kirar Hyundai da darajarta ya kai naira miliyan 5, ranar da aka dauke shi aiki a wata ma'aikata dake Victoria Island a cikin garin Legas.

An kama maigadi, Aba, a yankin Iyana Oworo a hanyar sa ta zuwa jihar Benuwe bayan da motar da ya sato ta mutu yana cikin tafiya, kamar yadda hukumar 'yan sanda a jihar Legas ta bayyana, ta bakin CSP Olusegun Ajamola, na ofishin'yan sanda dake Bar Beach.

Mai dokar bacci: Maigadi ya tafka sata ranar da aka dauke shi aiki

Mai dokar bacci: Maigadi ya tafka sata ranar da aka dauke shi aiki

Hukumar 'yan sanda ta bayyana cewar maigadi, Aba, ya aikata wannan halin bera ne ranar 30 ga watan satumbar da ya gabata. A ranar, mai laifin bayan da kowa ya tashi daga aiki, ya shiga dakin hutawar ma'aikata ya dauki makullin wata mota tare da wata na'ura mai kwakwalwa, sannan ya tuka motar da niyyar zuwa jihar Benuwe ya sayar da ita. Saidai maigadi, Aba, yayi rashin sa'a domin motar na dauke da matakan tsaro na zamani dake nuna duk inda take. 'Yan sandan sun ce suna samun rahoton satar motar daga kamfanin suka yi amfani fa fasahar tsaron dake jikin motar suka cimma mai laifin tun kafin ya fice daga kwaryar birnin Legas.

DUBA WANNAN: Kachikwu da Baru sunyi gum da bakin su bayan ganawa da shugaba Buhari da Osinbajo

A yayin binciken 'yan sanda, mai laifin ya amsa laifin sa, sannan ya bayyana cewar ya saci motar ne domin ya je jihar Benuwe yake haya da ita ko kuma ya sayar domin samun jarin fara yin sana'a.

Tuni dai ka gurfanar da Aba gaban kotun majistare dake Igbosere a jihar Legas bisa tuhumar aikata laifin sata. Saidai bayan an karantawa mai laifin tuhumar da ake yi masa, ya ce sam bai aikata wannan laifi ba. Mai shari'a, uwargida A.O Komolafe, ta amince da bayar da belin mai laifin akan kudi naira miliyan 2.5 ga duk wanda zai karbe shi, sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan nuwamba mai zuwa.

Yanzu haka dai maigadi, Aba, yana gidan yari kasancewar babu wanda ya gabata a kotu domin yin belin sa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel