Jirgin ruwa ya sake dilmiyewa da mutane 11 a jihar Kebbi

Jirgin ruwa ya sake dilmiyewa da mutane 11 a jihar Kebbi

Bayan kwanaki biyu da rasuwar mutane 18 a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku yayin safarar fasinjoji 18 daga kauyen Jeribago na jihar Kebbi zuwa kauyen Tuteku dake jihar Neja, mutane biyu sun sake rasa rayukansu a wani sabon hatsarin da ya afku a karamar hukumar Yauri dake jihar ta Kebbi.

A ranar Jumma'a ta yau, Musa Muhammad wanda shine ciyaman na karamar hukumar ta Yauri ya tabbatar da faruwa wannan ibtila'i, a wata ganawa da manema labarai na kamfanin dillancin labari na NAN.

A cewar ciyaman din, wannan jirgin ruwa ya bar kauyen Binua ne inda yake dauke da mutane 11 domin safararsu zuwa wata kasuwa da sai an ketare ruwa yayin da wannan hatsari ya faru.

Jirgin ruwa ya sake dilmiyewa da mutane 11 a jihar Kebbi

Jirgin ruwa ya sake dilmiyewa da mutane 11 a jihar Kebbi

"Akwai mutane biyu wata mata bafulatana tare da wani dattijo da suka rasa ransu yayin da jirgin ruwa ya dilmiye da su".

KARANTA KUMA: Rikicin Gabas ta tsakiya: Sarkin Saudiya ya ziyarci shugaban kasar Rasha domin ganawa da juna

Sai dai ciyaman din ya bayyana cewa, duk da cewar tsautsayi ba ya wuce ranarsa, akwai ganganci na matukin jirgin bisa kunnen kashi da yayi bayan hukumar kula da ruwa ta yi gargadin ma su safara a kan ruwa da su jinkirta zuwa wani lokaci na gaba.

Yayin da wannan jirgi ya dilmiya cikin ruwa ne wani karamin kwale-kwale ya kawo musu dauki inda kafin kowa ya ankara mutane biyu sun cika nan take sakamakon.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taron shugabanin kasashen duniya a kan dumaman yanayi

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taron shugabanin kasashen duniya a kan dumaman yanayi

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taro a kan dumaman yanayi
NAIJ.com
Mailfire view pixel