Kachikwu da Baru sunyi gum da bakin su bayan ganawa da shugaba Buhari da Osinbajo

Kachikwu da Baru sunyi gum da bakin su bayan ganawa da shugaba Buhari da Osinbajo

- Kachikwu da Baru sunyi gum da bakin su bayan ganawa da shugaba Buhari da Osinbajo

- Ganawar ta jagororin ma'aikatar man fetur na zuwa ne kwana uku bayan da Kachikwu ya aikewa shugaba Buhari takardar korafi a kan Baru

- Ana dai cigaba da cece-kuce a kan wasikar ta Kachikwu data sulale zuwa hannun manema labarai

Karamin ministan ma'aikatar man fetur, Emmanuel Ibe Kachikwu, yaki magana da manema labarai bayan ganawar sa da shuga Buhari a yau. Kachikwu ya isa fadar shugaban kasa da misalin karfe 11:35 na safe sanye cikin bakar kwat. Sannan ya bar fadar shugaban kasan bayan kamar ganawa sa'a guda.

Kachikwu da Baru sunyi gum da bakin su bayan ganawa da shugaba Buhari da Osinbajo

Kachikwu da Baru sunyi gum da bakin su bayan ganawa da shugaba Buhari da Osinbajo

Da fitowar Kachikwu ne manema labarai suka garzaya domin sanin yadda tattaunawar ta su ta kasance, amma sai Kachikwu ya kada baki ya ce "Babu magana".

Darektan hukumar ma'aikatar man fetur, Maikanti Baru, ya ziyarci mataimakin shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbajo, daidai lokacin da Kachikwu ke ganawa da shugaba Buhari, kuma kamar Kachikwu, Baru, yayi gum da bakin sa yayin da manema labarai suka tambaye shi abin da suka tattauna.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa reshen jihar Borno ya yanke jiki ya fadi matacce a masaukin sa

Wannan ganawa ta jagororin ma'aikatar man fetur na zuwa ne kwana uku bayan da Kachikwu ya aikewa shugaba Buhari takardar korafi a kan Baru.

Kachikwu ya zargi Baru da rashin yi masa biyayya tare da jingine shi gefe guda a kan harkokin dake faruwa a ma'aikatar ta man fetur.

Ana dai cigaba da cece-kuce a kan wasikar ta Kachikwu data sulale zuwa hannun manema labarai.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel