Toh fa: SERAP ta bukaci Buhari ya dakatar da shugaban NNPC, Maikanti Baru

Toh fa: SERAP ta bukaci Buhari ya dakatar da shugaban NNPC, Maikanti Baru

- Kungiyar SARAP ta bukaci shugaba Buhari ya gabatar da shugaban NNPC ga hukumomin EFCC da ICPC

- SARAP ta shawarci shugaban kasa ya dakatar da Mista Baru har bayan kammala bincike a kan zargin

- SERAP ta ce Idan ba a yi wani abu a kan zargin da Kachikwu ya yi ba, zai iya haifar da rashin yarda da gwamnatin tarayya

Kungiyar SARAP ta aika budedeyar wasika zuwa ga shugaba Muhammadu Buhari, kungiyar ta bukaci shugaban kasa ya yi amfani da ofishinsa da kuma matsayinsa na shugaba ya yi gaggawar gabatar da babban daraktan kamfanin albarkatun man fetur, NNPC, Mista Maikanti Baru a kan zargin cin hanci da rashawa zuwa ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC da hukumar ICPC don bincike, kuma idan akwai shaida a kan zargin, don ya fuskanci shari’a".

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, kungiyar ta kuma bukaci shugaba Buhari da ya dakatar da Mista Baru har zuwa lokacin da aka gabatar da shi ga EFCC da ICPC da kuma sakamakon binciken da hukumomi masu cin hanci da rashawa suka yi don kada a yi tunanin cewa gwamnati na daure masa gindi.

A cikin wasika da aka yi ranar 5 ga watan Oktobar 2017 wanda babban darektan kungiyar SERAP, Adetokunbo Mumuni, ya sanya hannu, ya bayyana cewa, "Zargin Dakta Kachikwu sun kasance manyan laifi wanda ta saba wa dokar cin hanci da rashawa da sauran ka'idojin 2000 da kuma yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan cin hanci da rashawa (UNAC) wanda Nijeriya ta amince da kwanan nan.

Toh fa: SERAP ta bukaci Buhari ya dakatar da shugaban NNPC, Maikanti Baru

Shugaba Muhammadu Buhari

KU KARANTA: Babachir da Baru suna wa Buhari 'aiki' ne don ya ci zaben 2019

Idan har ba a yi wani abu a kan zargin da Dokta Kachikwu ya yi ba, wannan zai iya haifar da rashin yarda da gwamnatin tarayya game da yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel