Babu bambamci tsakanin Musulman Arewa da na Kudancin kasar nan – Sheikh Dahiru Bauchi

Babu bambamci tsakanin Musulman Arewa da na Kudancin kasar nan – Sheikh Dahiru Bauchi

Shahararren Malamin addinin Musulunci Shehi Dahiru Usman Bauchi ya jaddada hadin kan Musulman Najeriya, inda yace babu wani bambaci tsakanin Musulman Arewa da na kudu.

Shehin Malamin ya bayyana haka ne yayin wani taron kungiyar Nasrul Lahi-L-Fatih (NASFAT), inda gudanar da addu’o’i ga Najeriya a bikin cika shekaru 57.

KU KARANTA: Alƙalin Alƙalai ya jagoranci tawagar Alƙalan kotun ƙoli zuwa fadar shugaban ƙasa

Shehin Malamin yace “ziyarar daya kawo jihar Legas na nuni ga hadin kan Musulman Najeriya, hakan na nufin babu rabuwar kai tsakanin Musulma Arewa da Musulman kudu.”

Babu bambamci tsakanin Musulman Arewa da na Kudancin kasar nan – Sheikh Dahiru Bauchi

Sheikh Dahiru Bauchi

Daga nan sai ya shawarci mahalarta taron da su cigaba da sadar da zumunci a tsakanin Musulmai, saboda dukkanin su yan uwan juna ne, ba tare da nuna bambamcin kabila ko yare ba.

Daga karshe Shehin Malamin ya yaba ma kungiyar NASFAT ta yadda suke watsa da’awar Musulunci a ciki da wajen kasar nan, tare da yi ma Najeriya addu’ar samun cigaba mai daurewa.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar NASFAT Imam Mahroof Onike AbdulAzeez ya gode ma Shehin Malamin daya samu halartar taron kungiyar, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel