Yadda tirela ta murkushe mutane 4 a kan wata babbar hanya

Yadda tirela ta murkushe mutane 4 a kan wata babbar hanya

Wani hatsarin sassafiyar yau da ya afku akan babbar hanyar jihar Legas zuwa Oyo, ya salwantar da rai daya tare da raunata mutane uku. Wannan hadarin ya faru ne sakamakon wata tirela da yi ram da motar dake dauke da wannan mutane.

Naij.com ta fahimci cewa wannan hatsarin ya faru ne a kusa da kasuwar Mil 12 dake garin Ogere, yayin da tirelar ta hadu da wata karamar mota kirar Toyota mai dauke da lambar AGL 743 EM.

Yadda tirela ta murkushe mutane 4 jihar Ogun

Yadda tirela ta murkushe mutane 4 jihar Ogun

Babatunde Akinyibi, wanda shine kakakin cibiyar kare cinkuso a kan manyan hanyoyi (Traffic Compliance and Enforcement, TRACE), ya tabbatar da faruwar wannan hadari.

KARANTA KUMA: NNPC: An hurowa Buhari wuta, Ko ina Dalar Amurka Biliyan 25 ta shiga?

Akinyibi ya bayyana cewa, tukin ganganci ne ya yi sanadiyar wannan hadari, inda ya kara tabbatar da cewa babbar motar tirelar ce ta sheka da karamar motar ta Toyota cikin wani rami

A kalamansa, "Karamar motar ta na dauke da mutane hudu, maza biyu mata biyu, inda guda daga cikin matan ta rasa rayuwar ta nan take, sai kuma sauran da suka samu munanan raunuka asibitin Skylark ya kawo musu dauki".

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel