Alƙalin Alƙalai ya jagoranci tawagar Alƙalan kotun ƙoli zuwa fadar shugaban ƙasa

Alƙalin Alƙalai ya jagoranci tawagar Alƙalan kotun ƙoli zuwa fadar shugaban ƙasa

A ranar juma’a 6 ga watan Oktoba ne shugaban kasa ya karbi bakoncin tawagar Alkalan kotun kolin kasar nan, a fadar shugaban kasa bayan ya halarci sallar juma’a.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Alkalin Alkalai, mai shari’a Walter Onnoghen ne ya jagoranci tawagar Alkalan, inda da isarsu, suka shiga ganawar sirri da shugaban kasa.

KU KARANTA: Yadda wani Ɗansanda ya halaka wani mutumi saboda an hana shi cin hancin naira 100

Alƙalin Alƙalai ya jagoranci tawagar Alƙalan kotun ƙoli zuwa fadar shugaban ƙasa

Alƙalin Alƙalai da Shugaban ƙasa

Majiyar NAIJ.com ta gano waus hotunan Alkalan da suka kai ziyarar, kamar yadda Kaakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya daura a shafinsa na Facebook.

Alƙalin Alƙalai ya jagoranci tawagar Alƙalan kotun ƙoli zuwa fadar shugaban ƙasa

Alƙalan kotun ƙoli a fadar shugaban ƙasa

Alkalan kotun sun hada da Ibrahim Tanko, Olabode Rhodes Vivour, Sylvester Ngwuta, Mary Ukaego Peter Odili, Olukayode Ariwoola, Musa Dattijo Muhammad, Clara, Bata Ogunbiyi, Kumai Bayang Akaahs, Kudirat Kekere-Ekun, John Inyang Okoro, Chima Centus Nweze, Amiru Sunusi, Amina Adamu Augie, Ejembie Eko, Paul Adamu Galinje da kuma mai shari’a Sidi Dauda Bage

Alƙalin Alƙalai ya jagoranci tawagar Alƙalan kotun ƙoli zuwa fadar shugaban ƙasa

Shugaban ƙasa

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da karamin ministan mai, Ibe Kachikwu, inda suka tattauna batun daya shafi karar shugaban NNPC daya kai. sai dai bai ce uffan bayan ganawar.

Alƙalin Alƙalai ya jagoranci tawagar Alƙalan kotun ƙoli zuwa fadar shugaban ƙasa

Alƙalan kotun ƙoli

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel