Harin 'yan ta'adda yayi sanadiyar mutuwar sojojin jamhuriyar Nijar dana kasar Amurka

Harin 'yan ta'adda yayi sanadiyar mutuwar sojojin jamhuriyar Nijar dana kasar Amurka

- Wani harin 'yan ta'adda da aka kai jiya alhamis a iyakar kasar Nijar da Mali yayi sanadiyar mutuwar sojoji 7

- An kaiwa sojojin harin​ kwanton baunar ne yayin da suke karbar horo daga wurin sojojin Amurka a kan yaki da ta'addanci

- Hukumar sojin Amurka dake Afrika ta bayyana daukar sojojinta da suka jikkata a harin zuwa kasar Jamus domin duba lafiyar su

Ma'aikatar tsaron kasar Nijar ta bayyana cewar wani harin 'yan ta'adda da aka kai jiya alhamis a iyakar kasar da Mali dake kudu maso yammacin​ Nijar, yayi sanadiyar mutuwar sojojin janhuriyar ta Nijar hudu da wasu karin sojoji uku na kasar Amurka.

Harin 'yan ta'adda yayi sanadiyar mutuwar sojojin janhuriyar Nijar dana kasar Amurka

Harin 'yan ta'adda yayi sanadiyar mutuwar sojojin janhuriyar Nijar dana kasar Amurka

Ma'aikatar tsaron ta bayyana kididdigar adadin sojojin da suka mutu a yau juma'a, sannan ta kara da cewar wasu sojoji guda 8 sun jikkata.

An kaiwa sojojin harin​ kwanton baunar ne yayin da suke karbar horo daga wurin sojojin Amurka a kan yaki da ta'addanci, kamar yadda ma'aikatar tsaron kasar Nijar ta bayyana.

DUBA WANNAN: Mabiya Shi'a sun bukaci shugaba Buhari ya bayyana dalilinsa na kin sakin Zakzaky

Shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou, yayin gabatar da jawabinsa a wani taron habaka tattalin arziki da ya halarta jiya a babban birnin kasar Nijar, Niamey, ya ce harin 'yan ta'addar ya jawo asarar rayuka da dama.

Maharan da suka zo cikin motoci 12 da babura 20 sun iske sojojin ne a daf da iyakar kasar Nijar da Mali mai nisan kilomita 200 daga Niamey. Iyakar dai dama tayi kaurin suna wajen aiyukan 'yan ta'addan kungiyar Al-Qaeda.

Hukumar sojin Amurka dake Afrika ta bayyana cewar ta dauke sojojinta da suka jikkata a harin zuwa kasar Jamus domin duba lafiyar su.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
INEC ta kori jami'anta 2 akan zargin yi wa gwamnan jihar Kogi rajista so biyu

INEC ta kori jami'anta 2 akan zargin yi wa gwamnan jihar Kogi rajista so biyu

INEC ta kori wasu jami'anta 2 akan yi wa gwamna Bello rajista so biyu
NAIJ.com
Mailfire view pixel