Shari'ar Diezani: Jami'an EFCC ne suka tursasa ni har na amsa cewa na karbi kudi N30m - Nwosu

Shari'ar Diezani: Jami'an EFCC ne suka tursasa ni har na amsa cewa na karbi kudi N30m - Nwosu

- Wani tsohon ma'aikaicin INEC mai suna Nwosu ya bayyana yadda EFCC ta tursasa ni amsa laifin karban naira miliyan 30 daga hannun Dieziani

- Ma'aikacin mai suna Nwosu ya yi ikirarin ta yi masa barazanar kulle ne idan bai amsa laifin ba

- Ya ce hukumar ta tursasa shi ya sallamar da kadaran sa na naira miliyan 30 da tsabar kudi naira miliyan 5

Wani tsohon ma'aikacin Hukumar Zabe ta Kasa wato INEC na Jihar Kwara , mai suna Christian Nwosu ya fada ma wani babban kotu a Legas yadda Hukumar EFCC ta tursasa shi ya amsa laifin morewa naira miliyan 30 daga hannun tshohuwar ministan Man fetur wato Dieziani Alison-Madueke.

Shari'ar Diezani: Jami'an EFCC ne suka tursasa ni har na amsa cewa na karbi kudi N30m - Nwosu

Shari'ar Diezani: Jami'an EFCC ne suka tursasa ni har na amsa cewa na karbi kudi N30m - Nwosu

Nwosu ya yi ikirarin shima tursasa shi aka yi ya sallamar da kadaran sa na kudi naira miliyan 30 da tsabar kudi naira miliyan 5. Ya fada ma Alkali Mohammad Idris cewan jami'in EFCC mai suna Usman Zakari ne ya yi masa barazanar kulle har sai ya amsa abun da hukumar ke son ji.

DUBA WANNAN: Patience Jonathan ta kai karar Magu da EFCC kotu, ta na neman diyyar naira biliyan 2

Nwosu ya ce daga nan ne sai jami'in tare da 'yan sandan mobayil suka tasa shi zuwa banki ya ciro naira miliyan 4 da sunan hukumar. Daga baya kuma su ka sa shi ya kara kawo naira miliyan 1.

A cewar Nwosu, jami'in ya ce masa babu abun da zai tseratar da shi sai amsa laifin karban naira miliyan 30. Idan kuwa ya ki basu hadin kai jami'in zai tabbata an daure shi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel