Babachir da Baru suna wa Buhari 'aiki' ne don ya ci zaben 2019 — PDP

Babachir da Baru suna wa Buhari 'aiki' ne don ya ci zaben 2019 — PDP

- Badakalar Baru da Kachikwu kamar ana hura wuta

- PDP ta ce ana sata ne don a sa Buhari ya ci zaben 2019

- APC ta karyata, ta ce PDP su kawo hujja

A jiya ne jam'iyyar PDP ta baiyana cewa manyan ma'aikatan gwamnati suna yin kwana da wasu kudaden ma'aikatu ana tarawa Buhari don ya ci zaben shugaban kasa a karo na biyu a 2019. Ta baiyana sunan tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, da kuma shugaban NNPC, Maikanti Baru a cikin wadannan ma'aikata.

Babachir da Baru suna wa Buhari 'aiki' ne don ya ci zaben 2019 — PDP

Babachir da Baru suna wa Buhari 'aiki' ne don ya ci zaben 2019 — PDP

Mai magana da yawun bakin PDP, Prince Dayo Adeyeye, ya ce in karya ne to Buhari ya umarci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da su binciki badakalar da ake yi a NNPC, karkashin Maikanti Baru inda dala biliyan $25 ta mila ta hanyar da bai kamata ba. Ta kuma ce Buhari ya sallami Baru din.

Wannan badakalar ta samo asali ne a lokacin da ministan kasa na man fetur, Ibe Kachikwu, ya aikawa Buhari wasika a kan Baru ya milar da kudeden nan ba ta hanyar da ya kamata ba. Wasikar kuma ta yi batan kai ta fada hannun baiyanr jama'a inda kowa ya ji labari.

Adeyeye ya ce, "In dai akwai irin su Abba Kyari a cikin kwamitin NNPC amma ana wannan badakalar bai ce komai ba, to mun tabbatar cewa Buhari ya san me ake yi kuma ya dauke kai saboda zaben shi na 2019 ake yiwa

"Wannan ba zancen batanci ba ne. Wasikar Kachikwu da ta fito fili ta nuna cewa lallai APC ba ta alkibla. Ta kau da ido wasu na lalube aljihwan kasar.

DUBA WANNAN: Harin 'yan ta'adda yayi sanadiyar mutuwar sojojin jamhuriyar Nijar dana kasar Amurka

"Muna maganar dala biliyan 25 ne fa. Duka-duka kudin makaman da Dasuki ya sace dala biliyan 2 ne kacal, amma an kama shi da mutane da dama saboda wannan badakalar."

Da aka nemi APC don a ji ta bakin ta, mai magana da yawun ta, Malam Bolaji Abdullahi, ya gaya wa manema labarai ta waya cewa "Wannan kawai batanci ne da PDP take yi. In kuma tana da hujjar ta na wannan batu, to ta fito da shi. Shin Buhari ya fito ya ce zai tsaya takarar 2019?"

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel