Kabilar Ibo: Kungiyar Ohanaeze ta yabi matasan arewa ta yadda suka mara ma zaman lafiya baya

Kabilar Ibo: Kungiyar Ohanaeze ta yabi matasan arewa ta yadda suka mara ma zaman lafiya baya

- Kungiyar kabilar Igbo mai suna Ohanaeze ta yabi matasan arewa ta yadda suka mara ma zaman lafiya baya

- Ta yi wannan yabo ne sakamakon tsayawa da Gamayyar Kungiyoyin Arewa ta yi kan yarjeniyar janye wa'adin da aka ba 'yan kabilar Igbo mazauna Arewa

- Kungiyar ta ce ta hayar zaman Lafiya da hadin kai ne ra'ayoyin 'yan kabilar Igbo zai samu karbuwa

A ranar Juma'a ne Kungiyar Matasan Kabilar Ibo ta Ohanaeze (OYC) ta yabawa Kungiyar Gamayyar Kungiyoyin Arewa bisa ga yadda ta tsaya kan yarjeniyar janye wa'adin da aka yanke ma 'yan kabilar Ibo mazauna Arewa na 1 ga watan Oktoba.

Idan mai karatu bai manta ba, wannan wa'adi ya tayar da hankula. Dalilin haka ya sa Kungiyoyin 2 suka yi ta zaman tattaunawa don neman sulhu.

Korar Kabilar Ibo: Ohanaeze sun jinjina wa matasan arewa domin nuna dattaku

Korar Kabilar Ibo: Ohanaeze sun jinjina wa matasan arewa domin nuna dattaku

A wani jawabi da mataimakin shugaban Kungiyar ta OYC mai suna Obinna Achuonye ya sa hannu, kungiyar ta yaba wa matasan Arewa kuma ta sakankace da ta hanyar hadin kai ne za'a kare ra'ayoyin 'yan kabilar Ibo musamman mazauna Arewacin Najeriya.

DUBA WANNAN: Shugaban NNPC ya ziyarci Osinbajo daidai lokacin da Buhari ke ganawa da Kachikwu

Kungiyar ta OYC ta kara da mika yabo da godiya ga dukkan Kungiyoyi da mutane da suka taimaka wurin tabbatar da zaman lafiya.

Ta kuma yi kira da a zauna lafiya musamman yadda zaben Gwamna na Anambra ke gabatowa a 18 ga watan Nuwamba na wannan shekara. Ta kuma yi kira ga Gwamnati da ta gyara manyan tituna na Kudu masa Gabas.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel