Rikicin Boko Haram ya maishe da yara 52,311 marayu - Shettima

Rikicin Boko Haram ya maishe da yara 52,311 marayu - Shettima

Akwai kimanin kananan yara 52, 311 na jihar Borno da rikicin Boko Haram ya jefa su cikin maraici sakamakon tayar da zaune tsayen 'yan kungiyar Boko Haram da ya addabi kasar nan musamman ma yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a ranar da gabata, in da ya kara da cewa akwai akalla mata 54, 911 da rikita-rikitar ta Boko Haram ta maishe su zaurawa.

A cewar gwamnan, da ba a yi gaggawar daukar wasu matakai ba akan wannan ibtila'i, to kuwa da yanzu wani labarin da ya sha ban-ban da wannan za a bayar musamman ma idan aka yi la'akari da yankin Arewa Maso Gabas.

Rikicin Boko Haram ya maishe da yara 52,311 marayu - Shettima

Rikicin Boko Haram ya maishe da yara 52,311 marayu - Shettima

Ya ke cewa, "idan mu kayi kuskuren rashin kulawa da wannan zaurawa da marayu ta hanyar kin tallafawa da muhallai da kuma abinda za su sanya a bakunan su, to tabbas shekaru 10 zuwa 15 masu gabatowa sai mun yi kuka da idanun mu".

KARANTA KUMA: 'Yan sandan jihar Ogun sun cafke miyagu 70 tare da manyan makamai

Gwamnatin jihar ta Borno ta dukufa wajen gine-ginen gidaje, makarantu, asibitoci da cibiyoyi daban-daban na cigaba da gudanar da rayukan al'ummomin jihar ta Borno.

Akwai kaulin da ya ke bayyana cewa, rikicin Boko Haram da ya kunno kai tun a shekarar 2009 ya salwantar da rayuka fiye da 20, 000 tare da sanya kimanin mutane miliyan 2.3 su yi hijira.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel