Yan bindiga sun yi awon gaba da wani Majistare a jihar Kogi

Yan bindiga sun yi awon gaba da wani Majistare a jihar Kogi

- Masu garkuwa da mutane sun sace wani majistare a Kogi

- Sun bukaci Iyalin sa su fanshe shi da Naira miliyan N100,000

- Kwamishinan yansadar jihar Kogi yace yansada suna kan binciken al'amarin

Yan Bindiga sun yi awon gaba da wani majistare a jihar Kogi, mai suna Mista Sam Unwchola akan hanyar Ajaokuta zuwa Lokoja.

Wani majiya mai karfi ya fada ma yan jaridar Daily Post cewa, yan bindigan sun sace majistaren ne a lokacin da yake dawowa daga wajen aikin sa tare da wani abokin sa mai sua Jimgbe a kusa da jam’iar Salem dake a Lokoja da misalin karfe 7pm na ranar Alhamis.

Yan bindigan sun bude wa majistare wuta kafin ya tsaya da motar sa.

Yan bindiga sun yi awon gaba da wani Majistare a jihar Kogi

Yan bindiga sun yi awon gaba da wani Majistare a jihar Kogi

Harbin da yan bindigan suka yi, ya samu abokin majistaren da suke cikin mota tare a idon sa na hannun hagu wanda yayi sanadiyar fashewar kumatin sa.

KU KARANTA : Biyafara : Rundunar sojin Najeriya ta yi magana game da inda Kanu yake

Mutanen da suke wajen bayan abun ya faru, sun garzaya da abokin zuwa wani asibiti dake kusa da Lokoja dan kulawa.

Hukumar sharia na Jihar Kogi ta tabbatar da aukuwan wannan lamari, sun fada ma yan jarida cewa yan bindigan sun kira matar majistaren da neman Naira miliyan N100,000 da za a fanshi ran sa da shi.

Kwamishinan yan sandar jihar Kogi, Mista Ali Janga y ace yanasanda suna kan bincke lamarin

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel