Shugaban NNPC ya ziyarci Osinbajo daidai lokacin da Buhari ke ganawa da Kachikwu

Shugaban NNPC ya ziyarci Osinbajo daidai lokacin da Buhari ke ganawa da Kachikwu

- Shugaban hukumar NNPC ya ziyarci mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yau

- A lokacin da ya kai ziyarar, Shugaba Buhari yana ganawa da karamin ministan man fetur, Ibe Kachiku

- Daga bisani mai kantoi Baru yayi sallar Juma'a tare da shugaba Buhari

Shugaban hukumar ma'aikatar man fetur, Maikanti Baru, ya ziyarci mataimakin shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbajo, yau a ofishin sa.

An dai tsinkayi Baru a ofishin mataimakin shugaban kasar ne a daidai lokacin da Shugaba Buhari ke ganawa da karamin ministan ma'aikatar man fetur, Emmanuel Ibe Kachikwu.

Shugaban NNPC ya ziyarci Osinbajo daidai lokacin da Buhari ke ganawa da Kachikwu

Shugaban NNPC ya ziyarci Osinbajo daidai lokacin da Buhari ke ganawa da Kachikwu

Hakazalika majiyar mu ta shaida mana cewar, Baru ya wuce ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba kyari, kafin daga bisani ya wuce zuwa masallacin juma'a inda shugaba Buhari yayi sallah.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa EFCC ke neman gurfanar da ni gaban shari'a - Patience Jonathan

A wata wasika data zirare zuwa ga manema labarai cikin satinnan, ministan ma'aikatar man fetur, Kachikwu, ya zargi shugaban ma'aikatar ta man fetur, Baru, da rashin yi masa biyayya, tare da bayar da kwangiloli na adadin dala biliyan 25 na bisa ka'ida ba, sannan ya bayyana cewar Baru ya jingine shi gefe guda a kan harkokin dake faruwa a ma'aikatar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel