Patience Jonathan ta kai karar Magu da EFCC kotu, ta na neman diyyar naira biliyan 2

Patience Jonathan ta kai karar Magu da EFCC kotu, ta na neman diyyar naira biliyan 2

- Ta shigar da karar hukumar EFCC da shugaban hukumar tana neman a biya ta diyyar naira biliyan 2 saboda cin zarafin da hukumar ke mata

- Ta roki kotun da ya furta cewan binciken da hukumar ke gudanarwa a kanta ba bisa ka'ida bane wanda hakan na taka hakkokinta

- Ta kuma ce ita 'yar kasuwa ce tun kafin shigar mijin ta siyasa

Patience matar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ta shigar da Magu da EFCC kotu tana neman a biya ta diyyar naira biliyan 2 na tauye hakkokinta da aka yi.

Ta shigar da wannan kara ne a wani babban kotu a Abuja ta na rokon kotun da ya furta cewan hukumar ta EFCC ta ci zarafi kuma ta bata mata suna ba tare da hukumar ta bi dokar kundin tsarin mulki ya tanadar ba.

Patience Jonathan ta kai karar Magu da EFCC kotu, ta na neman diyyar naira biliyan 2

Patience Jonathan ta kai karar Magu da EFCC kotu, ta na neman diyyar naira biliyan 2

Ta kuma bukaci kotun da ya hana hukumar ci gaba da taka hakkokinta. Wani lauyan Patience mai suna Sammie Somiari ne ya shigar da rubutacciyar karar a ranar 30 ga watan July.

DUBA WANNAN: Dalibi ya kwankwadi madarar fiya-fiya domin nuna kin amincewar sa da faduwa jarrabawa

Ta shigar da wannan kara ne sakamakon kunnin uwar shegu da hukumar ta yi wa karar da ta shigar a baya na neman hukumar ta daina taka hakkokinta.

Patience ta yi ikirarin tana da kasuwanci da take gudanarwa tun kafin mijin ta ya shiga siyasa. Ta kuma cigaba da tafiyar da suwancin ko da mijin nata ya zama shugaban kasa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel