'Yan sanda sun kama buhu 38 na tabar wiwi na kimanin kudi Naira miliyan 20 a jihar Legas

'Yan sanda sun kama buhu 38 na tabar wiwi na kimanin kudi Naira miliyan 20 a jihar Legas

Hukumar 'yan sanda ta jihar Legas ta kama buhu 38 na tabar wiwi sakamakon wani simame da ta yi a wasu yankuna da ake zarginsu da safarar miyagun kwayoyi da kayan maye, a yankin Itere da ke unguwar Mushin wanda akalla kudin su ya tashi Naira miliyan 20.

Naij.com ta ruwaito daga wata sanarwar kwamishinan 'yan sanda na jihar Edgal Imohimi, inda ya bayyana cewa akwai mutane 52 da hukumar ta cafke yayin simamen da ta kai wanda ake zarginsu da aikata wannan laifi sakamakon aiki da ya kaisu wajen wata tarzoma da tashi saboda wata mata da hakan ya yi sanadiyar lalatar motoci 150 a yankin.

A kalamansa, "a ta dalilin tsare-tsaren da na sanya a cikin al'ummomin yankin, mazauna yankin sun bayyana su suka bayyana maboyar wannan bata gari sakamakon hadin kai da muke samu daga al'ummar".

'Yan sanda sun kama buhu 38 na tabar wiwi na kimanin kudi Naira miliyan 20 a jihar Legas

'Yan sanda sun kama buhu 38 na tabar wiwi na kimanin kudi Naira miliyan 20 a jihar Legas

"Mun samu rahoton cewa masu fataucin kwayoyin da kayan maye sun addabi mazauna yankin na su wanda hakan ya sanya muka sita simame cikin kuma a ka yi nasarar cafke maza 44 da mata 8 tare da buhu 38 na tabar wiwi".

"Akwai wasu kayan maye da aka samu masu tsadar gaske wanda jimillan kudin su ya tashi Naira Miliyan 20.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya yi sababbin nadi a babban bankin Najeriya

Kwamishinan na 'yan sanda ya ci gaba da cewa, "na lura da yadda aikata wasu laifi suke alaka da fataucin miyagun kwayoyi da kayan maye, wanda hakan ya sanya mun nemi hadi gwiwa da sauran hukumomin tsaro musamman ma hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), domin hakan zai taimaka wajen rage faruwar laifuka".

"Ina kuma kara mika godiya ta ga mazauna da al'umomin yankin dangane da irin tallafawa da suke wajen fallasa duk wata maboya ta masu aikata laifi".

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel