Mabiya Shi'a sun bukaci shugaba Buhari ya bayyana dalilinsa na kin sakin Zakzaky

Mabiya Shi'a sun bukaci shugaba Buhari ya bayyana dalilinsa na kin sakin Zakzaky

- Mabiya Shi'a sun bukaci shugaba Buhari ya bayyana dalilinsa na kin sakin Zakzaky

- Kotu ta bada umarnin a saki Zakzaky amma har yanzu ba a sake shi ba

- Mabiya addinin suna kira ga a daina tauye musu hakkin su

Mabiya Shi’a sun kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya fadawa duniya dalilin da ya sa har yanzu shugaban kungiyar su Ibrahim Zakzaky yake a kulle.

Kungiyar ta kara dagewa akan sai an saki shugaban ta domin kuwa hakkin su ne kuma a kan dai-dai suke tafiya a tafarkin addinin su. Shugaban yada labaran kungiyar, Ibrahim Musa ne ya aika sakon su zuwa ga jaridar Daily Post.

'Yan Shi'a na so Buhari ya fada musu dalilinsa na kin sakin Zakzaky

'Yan Shi'a na so Buhari ya fada musu dalilinsa na kin sakin Zakzaky

Duk da cewa Kotu ta bada umarnin a bada belin Zakzaky, Minista Lai Mohamed ya ce bai ga dalilin da zai sa a saki Shugaban nasu ba. A wata ganawa da aka yi da Ministan a sashin Hausa na BBC ya ce zaman Zakzaky a rufe shine daidai saboda wasu dalilan tsaro da bai bayyana ba. Kuma zaman shi a tsare shine zai samarwa da mutanen kasa zaman lafiya.

'Muna bukatar Ministan ya fito ya shaidawa duniya dalilin da ya sa baza su saki Zakzaky ba da dalilin da ya sa suke cewa zai kawo rashin kwanciyar hankali a kasa' inji mabiya Shi'a.

Tun bayan tsare shin da sojin tayi bayan gumurzun da suka yi da babban hafsan Soji Janar Tukur Buratai sun shaidawa kotu an tsare shi ne ba don ya aikata laifi ba.

DUBA WANNAN: Za a sayar da filayen jirgin sama-Hadi Sirika

Bayan da Kotu ta bada umarnin a bada belin sa da biyan sa diyya amma duk da haka ba a sake shi ba. Gwamnatin Buharin ta amince da ta sake shi da gina mishi sabon gida, amma sun nuna cewa mutane da yawa basa so su rabe shi a matsayin makwabta, 'wannan shine dalilin da ya sa muke so Lai Mohamed ya fadi dalilin da ya sa suke ganin cewa Sheikh Zakzaky fitina zai zame wa al’umma' mabiya shi'a sun kara jaddadawa.

A karshe mabiya addinin suna kira ga gwamnatin da tayi gaggawar sakin Shugaban su da sauran ‘yan uwansu da suka tsare . Kuma suna kara shaidawa cewa hakkin su ne da su gudanar da addinin su yadda suke so a cikin kwanciyar hankali.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel