Za mu dauki ma'aikatan kiwon lafiya 1,000 a jihar Kaduna - Kwamishinan Lafiya

Za mu dauki ma'aikatan kiwon lafiya 1,000 a jihar Kaduna - Kwamishinan Lafiya

- Jihar Kaduna zata dauki ma'aikatan kiwon lafiya 1,000

- Kwamishinan ya shaida dalilin hakan domin rage matsalolin da mata ke fuskanta a asibitocin gwamnati ne

- Gwamnatin zata tallafawa masu fama da ciwon suga da hawan jini

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Kaduna Dr. Paul Dogo ya bada sanarwar cewa gwamnatin jihar zata dauki ma’aikatan kiwon lafiya 1,000 a don bunkasa yankin kiwon lafiya.

'Daga cikin ma’aikatan an bawa ma’aikata 418 takardar daukar aiki, tuni sun fara gudanar da aikin su, sauran ma’aikatan kuma za su fara daga baya' ministan ya shaida.

Za mu daukin ma'aikatan lafiya 1,000 a jihar Kaduna - Kwamishinan Lafiya na Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai

Ma’aikatan da aka dauka sun hada da likitoci 100, nas-nas, masu bada magunguna, masu aikin dakin gwaje-gwaje 30, masu aikin abinci 20 da likitocin hakori. Ma’aikatan zasu fara aiki a asibitocin gwamnati na jihar manya da kanana.

A farkon shekarar nan ne gwamnatin jihar ta shaida cewa zata dauki ma’aikatan kiwon lafiya domin kawo karshen kalubalen da mata ke fuskanta a asibitocin gwamnati.

DUBA WANNAN: 'Yan Najeriya sun hada kai don samun galaba a kan Boko Haram

Ministan ya kara shaidawa yadda gwamnatin jihar ta dauki ma’akata 200 da zasu kula da masu fama da ciwon suga da hawan jini. Gwamnatin zata bawa masu ciwon sugan kulawa kyauta. Marasa lafiyan da gwamnatin zata bawa kulawa manya ne da suka haura shekaru 70.

A cikin shekarar nan gwamnatin jihar ta dau alwashin gyara kananan asibitoci da suka lalace domin mutane su sami ingatacciyar lafiya. A yanzu haka an gyara 11 daga cikin 255 da gwamnatin zata gyara.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel