Muna magance matsalolin da suke iyakokin kasa, Inji Osinbajo

Muna magance matsalolin da suke iyakokin kasa, Inji Osinbajo

- Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya na kokari matuka wurin toshe kafofin barna a bakin iyakoki

- Ya ce gwamnatin Buhari tana da kudirin farfado da kuma bunkasa masana'antu a kasan nan

Mataimakin Shuganan Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jaddada kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi don magance shigo da gurbatattun kaya da shigo da kaya ta barauniyar hanya a iyakokin kasa.

Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin tarban wakilan Kungiyar Masana'antu Kasa Najeriya (MAN) a fadar shuganan kasa.

Muna magance matsalolin da suke iyakokin kasa, Inji Osinbajo

Muna magance matsalolin da suke iyakokin kasa, Inji Osinbajo

An samu ta hannun babban mai ba Osinbajo shawara kan harkan labarai mai suna Laolu Akande, Osinbajo ya ce akwai bukatan a tsananta dokoki a bakin iyakoki don bunkasa kayan da aka sana'anta a cikin gida Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Dalibi ya kwankwadi madarar fiya-fiya domin nuna kin amincewar sa da faduwa jarrabawa

Osinbajo ya ce an zuba isassun jam'an tsaro a iyakokin kuma za'a hada gwiwa da gwamnatin makotan kasashe don karin tsaro. Bisa roko daga kungiyar, Osinbajo ya ce gwamnati zata rika sayen kayakin da aka sana'anta a Najeriya.

Osinbajo ya ce gwamnatin Buhari tana bada muhimmanci wurin farfado da masana'antu da kasuwanci. Shi kuwa shugaban kungiyar mai suna Dakta Frank Udemba cewa ya yi hakan zai samar wa 'yan Najeriya aikin yi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel