An kama shugaban matan jam'iyyar APC cikin almundahanar N1.5m

An kama shugaban matan jam'iyyar APC cikin almundahanar N1.5m

A ranar Alhamis din da ta gabata ne wata babbar kotun birnin Benin dake jihar Edo, ta gurfanar da shugabar mata ta jam'iyyar APC Dakta Aisosa Amadasum, tsohon ciyaman na cibiyar ilimi (State Universal Basic Education Board, SUBEB) Prince Stephen Alao, tare da wasu manya uku na cibiyar ta ilimi.

Kotun ta gurfanar da wadannan mutane biyar bisa laifin yin sama da fadi da Naira Biliyan 1.5 wanda hukumar EFCC take zarginsu da yi, wanda lauyan na hukumar ta EFCC Ben Ubi ya nuna rashin goyon bayansa bisa beli da lauyan wandanda ake tuhuma ya nema.

Sakamakon almundahanar Naira Biliyan 1.5 wasu manya 5 na kasar nan sun gurfana

Sakamakon almundahanar Naira Biliyan 1.5 wasu manya 5 na kasar nan sun gurfana

Naij.com ta fahimci cewa, ana zargin wadannan mutane biyar bisa aikata laifin yin bushasharsu da kudin hannayen jari na cibiyar ta SUBEB da su ka sayar, wanda wannan laifi da suka aikata ya saba dokar cin hanci da rashawa karkashin sashe na 26 da aka zartar a shekarar 2000.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya yi sababbin nadi a babban bankin Najeriya

Akwai Adams Osabuohien, Dove Momodu da Mallam Ali Sulayman wanda kotun ta gurfanar bisa sanya hannayensu wajen aikata wannan laifi.

Duka su biyar din sun aikata wannan laifin ne a yayin da suke shugabanci cibiyar ta SUBEB a shekarar 2016, yayin da hukumar EFCC ta caraf da su a ranar 22 ga watan Nuwamba na shekarar 2016.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel