An kulle Babban Asibiti wanda darajarsa ya kai naira biliyan 41 a Akwa Ibom

An kulle Babban Asibiti wanda darajarsa ya kai naira biliyan 41 a Akwa Ibom

- Dominic Ukpong wanda shi ne Kwamishinan Kiwon lafiya na Jihar ne ya sanar da kulle asibitin

- Kwamishinan ya ce an kulle asibitin ne sakamakon sabani da aka samu tsakanin gwamnatin Jihar da sashin kula da cututtukan zuciya na asibitin

- Sashin sun yi korafin gwamnatin Jihar ta gaza sauke nauyin da ya raytaya a wuyan ta

An rufe babban asibitin Uyo na Jihar Akwa Ibom da aka kaddamar shekaru 2 da suka wuce karkashin mulkin tsohon gwamnan Jihar wato Godswill Akpabio.

Jaridar Premium Times ta bada rahoton cewa mafi yawan ma'aikatan asibitin baki ne 'yan kasan Indiya. An samu labarin cewa shi kuwa Akpabio ya yi alfaharin babu kamar asibitin a inda ya fi asibitocin koyarwa a fadin kasan nan kayan aiki.

An kulle Babban Asibiti wanda darajarsa ya kai naira biliyan 41 a Akwa Ibom

An kulle Babban Asibiti wanda darajarsa ya kai naira biliyan 41 a Akwa Ibom

NAIJ.com ta samu labari cewan a ranar Laraba 4 ga wannan wata ne Kwamishinan kiwon Lafiya na Jihar wato Dominic Ukpong ya tabbatar da rufe asibitin sakamakon sabani tsakini gwamnatin Jihar da sashin kula da cututtukan zuciya na asibitin.

DUBA WANNAN: An yi ram da wani ma'aikaci da ya sace kayan aiki na naira miliyan 40

Kwamishinan a nasa fahimtar, hukumar asibitin ba su gamsu da yadda gwamnati ke kula da asibitin bane. Ya ce shi kuwa shaida ne kan yadda gwamnati ke bada makudan kudi ga masu kula da asibitin domin kulawar.

A cewar Kwamishinan, asibitin an gina shi ne akan kudi kimanin naira bilyan 41.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel