Badakalar NNPC: Buhari da Kachikwu na cikin ganawar sirri

Badakalar NNPC: Buhari da Kachikwu na cikin ganawar sirri

- A yanzu haka, shugabna kasa Muhammadu Buhari tare da karamin ministan man fetur, Ibe Kachikwu na cikin ganawa

- Kachikwu ya zargi shugaban na NNPC da aikata rashin da’a ga hukumar ma’aikatar mai ta kasa

- An ce Ministan ya isa ofishin shugaban kasa da misalin karfe 11:40 na safe

A yanzu haka, shugabna kasa Muhammadu Buhari tare da karamin ministan man fetur, Ibe Kachikwu na cikin ganawa kan wasikar dake zargin shugaban rukunin kamfanin NNPC, Mikanti Baru da aikata rashawa.

Ministan ya isa ofishin shugaban kasa da misalin karfe 11:40 na safe.

Kachikwu ya zargi shugaban na NNPC da aikata rashin da’a ga hukumar ma’aikatar mai ta kasa, wanda ministan ke shugabanta.

KU KARANTA KUMA: PDP ta bukaci Buhari da yayi gaggawan dakatar da Maikanti Baru

Ministan, a cikin wani wasika da ya bazu, ya sanar da shugaba Buhari akan tsarin, an bayar da kwangilar makudan kudade har dala biliyan 25 ba tare da an sanar dashi ko hukumar ta NNPC ba.

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel