Mutane shidda sun mutu an wani hari da makiyaya suka kai jihar Delta

Mutane shidda sun mutu an wani hari da makiyaya suka kai jihar Delta

- Mutane shidda ne suka mutu a wani sabon hari da ake zargin makiyaya sun kai jihar Delta

- An yi asarar albarkattun gona na miliyoyin naira

- Kakakin rundunar yan sandan jihar, Mista Andrew Aniamaka ya karyata al’amarin

Akalla mutane shidda ne suka mutu a wani sabon hari da ake zargin makiyaya ga kaiwa garin Obodogba, Okpanam, karamar hukumar Arewacin Oshimili na jihar Delta.

Jaridar Guardian ta tattaro cewa al’amarin wanda ya afku a safiyar jiya, Alhamis, 5 ga watan Oktoba ya sanya al’umman Okpanam cikin alhini, musamman sashin Obodogba inda shanayen makiyayan suka lalata albarkatun gona da ya kai kimanin miliyoyin naira.

Koda dai kakakin rundunar yan sandan jihar, Mista Andrew Aniamaka ya karyata al’amarin a matsayin babu gaskiya, kungiyar Ugoani na Okpanam, wanda suka tabbatar da al’amarin sun bayyana cewa an aika takardan korafi ga hedkwatan rundunar yan sanda a Asaba kan mamayar da makiyaya suka kai gonakin al’umman Obodogba, cewa mutane shidda sun rasu a mamayar.

KU KARANTA KUMA: Badakalar NNPC: Buhari da Kachikwu na cikin ganawar sirri

An tattaro cewa rikici ya fara ne lokacin da wasu mazauna Obodogba suna gano cewa makiyaya sun kai ma gonakin su hari don lalata masu shukokinsu da shanayen su.

Wannan yasa mutanen suka kalubalanci wadanda suka kai harin amma sai sukayi barazanar kashe mutanen da makamansu, sai gashi labara yazo a jiya cewa gonakin da fadan ya kaure yayi sanadiyar mutuwar mutane shidda.

A halin da ake ciki jami’an yan sanda a sashin Okpanam, wadanda suka nemi a boye sunansu sunce an kama biyu daga cikin makiyayan, inda suka kara da cewa a yanzu suna taimaka wa yan sanda wajen cigaba da bincike.

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel