Biyafara : Dattawan yankin Arewa na tsakiya da na Kudu sun caccaki gwamnatin tarayya akan ayyana IPOB a matsayin yan ta’ada

Biyafara : Dattawan yankin Arewa na tsakiya da na Kudu sun caccaki gwamnatin tarayya akan ayyana IPOB a matsayin yan ta’ada

- Kungiyar dattawa Arewa na tsakiya ta soki gwamnatin tarayya akan ayyana kungiyar IPOB a matsayin yan ta'adda

- Kungiyar sun bukaci gwamnatin tarayya ta daina amfanin da sojoji wajen magance rikicin farar hula

- Dattawan yankin Arewa na tsakiya da na Kudu sun gana da juna a Abuja

Kungiyan dattawan Arewa na tsakiya da na Kudu sun caccaki gwamnatin tarayya akan ayyana kungiyar yan asalin Biyafara IPOB a matsayin yan ta’adda.

A wata taro da suka yi a ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja, kungiyar ta ki amincewa da laka wa kungiyar IPOB sunan yan ta’adda da gwamnati tarayya ta yi.

A cikin wadanda suka halarci taron ya kunshi Cif EdwinClark, Barnabas Gumade, Jerry Gana, Olu Falae, Tunde Ogbeha, Ayo Adebajo, Yinka Odumakin, Dan Suleiman da Stella Omu.

Biyafara : Dattawan yankin Arewa na tsakiya da na Kudu sun caccaki gwamnatin tarayya akan ayyana IPOB a matsayin yan ta’ada

Biyafara : Dattawan yankin Arewa na tsakiya da na Kudu sun caccaki gwamnatin tarayya akan ayyana IPOB a matsayin yan ta’ada

“Kungiyar ta yi kira da gwamnatin tarayya da ta daina amfani da sojoji wajen magance rikicin farar hula, saboda a kowani dimokardiyya yansanda ake amfani da su wajen magance matsalolin da ya shafin farar hula.

KU KARANTA : Biyafara : Rundunar sojin Najeriya ta yi magana game da inda Kanu yake

“Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da attisayn da za ta tura sojoj yankin kudu maso kudu da kudu maso yamma yi, saboda yankin su akawai zaman laifiya.”

Kungiyar sun kai wa gwamnatin tarayya kukan su akan rikicin manoma da makiyaya da matsalar ma su garkuwa da mutane da ya addabi yankin Arewa na tsakiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel