Wata mata ta watsa wa mijinta tafasasshen ruwan barkono a gabansa saboda sabani da suka samu

Wata mata ta watsa wa mijinta tafasasshen ruwan barkono a gabansa saboda sabani da suka samu

- Kotu ta gurfanar da wata mata bisa zargin yunkurin kashe mijinta

- Ta zuba wa mijin nata tafashahhen ruwan barkono a gaban sa

- Alkalin kotun ya bayar da belin matar akan kudi naira dubu dari

Kotun dake zaune a yankin Ebute Metta na jihar Legas ta kama da wata mata, Ngozi Obasi, mai shekaru 31 a duniya bisa zargin yunkurin kashe maigidanta, Igwe Obasi, ta hanyar zuba masa tafashasshen ruwan barkono a gaban sa.

‘Yar sandar da ta shigar da karan Kehinde Omisakin ta cewa Ngozi ta aikata wannan mummunan laifi ne a ranar 1 ga watan Oktoba da misalin karfe uku na dare a cikin gidansu dake titin Fatiregun St.Ilaye a Ebute Meta bayan wata ‘yar sabani da ta shiga tsakaninsu.

KU KARANTA KUMA: Abdullahi Sugar ya goyi bayan Atiku da ya tsaya takarar shugabancin kasa a 2019

Wanda ta shigar da kara ta ce aikata irin hakan ya saba wa doka ta 230 na kundin tsarin mulkin jihar da ya shafi aikata irin wadannan laifuffuka. Duk da cewa kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa aikata irin wannan laifin kan sa a daure mutum a kurkuku har sai gawa.

Alkalin kotun Tajudeen Elias ya bayar da belin matar akan kudi naira 100,000 tare da shaidar takardan biyan haraji ga gwanatin jihar Legas na tsawon shekaru uku sannan ya daga sauraron karan zuwa ranar 16 ga watan Oktoba.

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel