PDP ta bukaci Buhari da yayi gaggawan dakatar da Maikanti Baru

PDP ta bukaci Buhari da yayi gaggawan dakatar da Maikanti Baru

- Jam’iyyar PDP ta yi kira ga shugaba Buhari da yayi gaggawan dakatar da Maikanti Baru

- Kiran ya biyo bayan wasikar da karamin ministan man fetur ya aika wa shugaban kasar

- Jam’iyyar ta kalubalanci shugaban kasa da ya tabbatar da cewa yaki da rashawarsa gaskiya ce ta hanyar hukunta Baru

Babban jam’iyyar adawa ta kasa wato PDP tayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta daukar mataki akan shugaban kamfanin NNPC, Maikanti Baru ta hanyar dakatar da shi.

Wannan kira ya biyo bayan bayyanar wasikar da karamin ministan mai, Ibe Kachikwu ya aika ma shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya zargi Maikanti Baru da bayar da kwangila na makudan kudi ba bisa ka’ida ba.

Kakakin jam’iyyar ta PDP, Dayo Adeyeye a wata sanarwa da ya saki yace kamata yayi shugaba Buhari ya dauki mataki akan al’amarin wanda hakan ne zai nuna cewa lallai yana yakar cin hanci da rashawa amma sai gashi yayi burus da lamarin.

KU KARANTA KUMA: Abdullahi Sugar ya goyi bayan Atiku da ya tsaya takarar shugabancin kasa a 2019

Don haka sunyi kira ga shugaban kasa da ya binciki Maikanti Baru sannan kuma a hukunta shi idan har aka same shi da aikata abunda aka zarge shi a kai. A cewar su hakan zai tabbatar da cewa ba yan jam’iyyar su kadai ake wa bita da kulli ba.

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel