Hukumar kididdiga ta fitar da yawan kudin da aka samu tun da aka fara hakar mai a kasar nan

Hukumar kididdiga ta fitar da yawan kudin da aka samu tun da aka fara hakar mai a kasar nan

Tun a sanda aka fara hakar mai don kudi a Najeriya a 1961, Najeriya ke amsar makudan kudade da take amfani dasu wajen shigar da kayan abinci da sauran bukatu, kasar kuma ta dogara ne da man kacokan tunda ta watsar da sauran sana'o'i na masana'antu da noma. Yanzu dai jiki magayi.

Kididdigar da hukumar ta fitar a jiya, Naira tiriliyan dari da sha uku Najeriya ta samu daga fitar da man fetur. Wato naira miliyan sau dubu, sau wata dubun, sau wata dari da sha ukku. N113,000,000,000,000 kenan. Kamar dai malala gashin tinkiyoyi.

Hukumar kididdiga ta fitar da yawan kudin da aka samu tun da aka ara hakar mai a kasar nan

Hukumar kididdiga ta fitar da yawan kudin da aka samu tun da aka ara hakar mai a kasar nan

Sai dai kamar ba haka yake a kas ba, domin banda bakin talauci, babu inda jama'ar kasar nan suke jin wani sanyi-sanyi. Hakan kuma yana ta'allaka ne da mulkin sojoji, wadanda suka yi mulki babu wanda ya isa ya tuhume su yadda suke kashe kudi, da ma na 'yan siyasa, masu ciki baka ciki rumbu.

A cikin rahoton, A shekarar 2005 ne aka i fitar da mai mafi yawa, haka kuma a 1961 ne aka itar da maffi karanci.

DUBA WANNAN: Aisha Ahmad, sabuwar Amarya a gwamnatin APC ta Buhari

Gangar mai biliyan 33 dai aka tono daga karkashin kasar Najeriya, wasunsu a kan doron kasa a rijiya, wasu a kasan teku.

Rahoton bai fadi ko harda arzikin gas da sauran dangogi da aka samu ba, sai dai ya ce daga hukumar NNPC aka kwakulo bayanan.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Dakin Nnamdi Kanu bayan harin soji, a Naij.comTV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel