Biyafara : Rundunar sojin Najeriya ta yi magana game da inda Kanu yake

Biyafara : Rundunar sojin Najeriya ta yi magana game da inda Kanu yake

- Rundunar Sojin sun bukaci yan Najeriya su tambayi iyalan Nnamdi Kanu game da inda ya ke

- Sani Kukasheka ya ce mabiyan Nnamdi Kanu suna cikin tsaka mai wuya

- Nnamdi Kanu yayi amfani da farfaganda wajen yaudarar mutane da ikrarin neman yancin Biyafara

Mai magana da yawun bakin rundunar sojin Najeriya, Sani Usman Kukasheka, yace iyalan shugaban kungiyar yan asalin Biyafara, Nnamdi Kanu sun san inda ya boye.

Brigediya Janar Usman Sani Kukasheka ya bukaci yan Najeriya da su tambayi dan uwan shugaban kungiyan yan asalin Biyafara IPOB Ifeanyi Ejiofor inda Nnamdi Kanu yake.

Biyafara : Rundunar sojin Najeriya ta yi magana game da inda Kanu yake

Biyafara : Rundunar sojin Najeriya ta yi magana game da inda Kanu yake

Sani Usman ya ce shugaban IPOB, Nnamdi Kanu mutum ne wanda ba shi da abun yi, wanda yayi amfani da farfaganda wajen yaudarar mutane da ikrarin neman yanci Biyafara.

KU KARANTA : Wani mutum ya yi wa diyar matar sa mai shekaru 13 ciki

Sani Usman ya bayyana haka ne a Abuja a lokacin da ya zantawa da manema labaru a ranar Alhamis. Usman yace mabiyan Nnamdi Kanu suna cikin tsaka mai wuya.

Mai magana da yawun bakin rudunar ya tabbatar wa ya Najeriya cewa shugaban IPOB Nnamdi Kanu ba ya hanun sojojin Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel