NNPC: An hurowa Buhari wuta, Ko ina Dalar Amurka Biliyan 25 ta shiga?

NNPC: An hurowa Buhari wuta, Ko ina Dalar Amurka Biliyan 25 ta shiga?

Tun a ranar da gabata, shugaban kasa Muhammadu Buhar ya shiga fuskantar kalubale domin fayyace yadda aka yi kasafin Dalar Amurka Biliyan 25 na kudin da kamfanin man fetur na kasa (NNPC) ya salwantar.

Naij.com ta ruwaito tun cikin makon nan cewa, karamin ministan man fetur Ibe Kachickwu ya rubuta wasika zuwa ga shugaba Buhari kan yadda shugaban NNPC Maikanti Baru ya ganin damar sa da wannan makudan kudi.

NNPC: An hurowa Buhari wuta, Ko ina Dalar Amurka Biliyan 25 ta shiga?

NNPC: An hurowa Buhari wuta, Ko ina Dalar Amurka Biliyan 25 ta shiga?

Rahotanni daga shafin The Nation sun bayyana cewa, ministan ya yi kokarin ganawa da shugaban kasar a ranar Alhamis din da ta gabata domin gano bakin zaren da jin yadda Baru ya ke yin gaban kansa da al'amurran kamfanin na NNPC, sai dai wannan ganawa ba ta yiwu ba inda ake sa ran a yau Jumma'a za su hadu a fadar ta shugaban kasa dake birnin tarayya.

KARANTA KUMA: Labari Cikin Hotuna: Hukumar 'Yan sanda ta sake damkar masu garkuwa da mutane a jihar Kaduna

Kungiyar kwadago NLC, jam'iyyar PDP da wadansu cibiyoyi da kungiyoyi da dama na kasar nan sun bukaci shugaban kasar ya titsiye Baru domin jin yadda yake gudanar al'amurran kamfanin ba tare da neman izini da yardar magabatansa ba.

Wadansu kungiyoyi da hukomomin ma su na bukatar shugaban kasar ya dakatar da Baru sannan kuma a fede ma sa biri har wutsiya kamar yadda ake yiwa Sambo Dasuki kan kudin makamai, ya yin da hukumar EFCC da ICPC suke yunkuri domin a basu damar far gudanar da bincike kan yarda irin wanna makudan kudi su ke shirwa.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel