An kama wani ‘Dan Najeriya da Safarar miyagun kwayoyi a wata kasa

An kama wani ‘Dan Najeriya da Safarar miyagun kwayoyi a wata kasa

- Wani ‘Dan Najeriya ya buge da harkar kwayoyi a kasar waje

- Wannan ta’aliki ya tafi kasar wajen ne da niyyar karatun Boko

- Yanzu haka dai an shiga Kotu da shi domin ana gwabza shari’a

Mun samu labari daga wata Jarida mai suna The Canberra Times cewa wani ‘Dalibin Najeriya ya shiga uku bayan an kama sa da miyagun kwayoyi masu yawa a wata kasar Turai.

Wannan abu ya faru ne a Garin Australia da wani mai suna Jackson Igwebuike wanda ya ke karatun Digirgir. Wannan mutumi ya shigo da kwayoyi cikin kasar ne har na Dala Miliyan 10 sai dai bai yi nasarar wucewa da su. An samu kwayoyin ne cikin wani karfe mai siffar kifi.

KU KARANTA: An dakatar da Shugaban NHIS daga aiki

Jami’an Kasar sun bayyana cewa kwayoyin da saurayin ya dauko su na da illa ga Jama’a. Yanzu haka dai an shiga Kotu da wannan Dalibi inda aka same shi da laifi. Ana dai iya daure wannan matashi har karshen rayuwar sa a kasar idan ya taki sa’a.

Dazu kun ji cewa masu garkuwa da mutane sun kashe Farfesa Paul Otasowie na Jami’ar Birnin Benin ta Tarayya watau UNIBEN inda a nan wancan yaron yayi Digirin san a farko.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel