Manyan jami’an gwamnati sun hadu akan zargin zambar dala biliyan 25 a NNPC

Manyan jami’an gwamnati sun hadu akan zargin zambar dala biliyan 25 a NNPC

- Badakalar kwangilan dala biliyan 25 dake gudana yanzu a NNPC ya billo ne bayan wani wasika da Ibe Kachikwu ya aika ga shugaba Buhari ya terere

- Wasikar da yayi yamadidi ya tattaro cece-kuce a tsakanin yan siyasa wadanda sukayi kira ga shugaban kasa da ya dauki mataki a kan zargin rashawar

Wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati da makusantan shugaba Muhammadu Buhari sun gudanar da wani taro kan badakalar dala biliyan 25 da ya billo a kamfanin NNPC.

Badakalar ya billo ne bayan karamin ministan man fetur, Ibe Kachikwu a cikin wani wasika da ya aika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 30 ga watan Agusta yayi terere, inda ya zargi manajan darakta na kamfanin NNPC, Dr. Maikanti Baru da rashin da’a da kuma rashawa.

Ministan ya bayyana cewa Baru da bayar da kwangila komanin dala biliyan 25 ko naira triliyan 9 wanda ya rinjayi farashin dala akan N360 ko wani dala, inda yayi gargadin cewa ba karamin barna al’amarin zaiyi ba idan har aka bar shi.

Wasikar wanda ya karade yanar gizo a ranar Talata, ya janyo cece-kuce a tsakanin yan siyasa wadanda sukayi kira ga shugaban kasa da ya dauki mataki a kan zargin rashawar.

KU KARANTA KUMA: Abdullahi Sugar ya goyi bayan Atiku da ya tsaya takarar shugabancin kasa a 2019

Sahara reporters ta wallafa a shafinta na twitter a ranar Juma’a, 6 ga watan Oktoba, cewa wasu daga cikin mataimakan shugaban kasa sun gana akan badakalar.

A cewar shafin ta yanar gizo, wadanda suka halarci ganawar sun hada da, Mamman Daura, kawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Isa Funtua, wanda ya kasance tsohon abokin shugaban kasar, Gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun da kuma shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki.

Sai dai ba’a bayyana abunda ganawar ta kunsa ba tukuna.

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel