Wasu ‘Yan bindiga sun kashe wani babban Malamin Jami’a

Wasu ‘Yan bindiga sun kashe wani babban Malamin Jami’a

- Wani Farfesa ya bakunci lahira bayan da ‘Yan bindiga su ka harbe sa

- Hakan ya zo ne bayan da farko an sace babban malamin makarantar

- Jami’an ‘Yan Sanda sun ce an kama wasu da ake zargi da hannu ciki

Mun samu labari daga Jaridun kasar nan irin su Vanguard cewa a can Garin Benin an sace wani Malamin Makaranta da ake ji da shi wanda daga karshe kuma aka kashe shi.

Masu garkuwa da mutane ne su ka sace Farfesa Paul Otasowie na Jami’ar Birnin Benin ta Tarayya watau UNIBEN inda daga karshe karshe su ka harbe shi. Babu dai abin da wadannan mutane su ka nema daga hannun Malamin.

KU KARANTA: Talauci ya sa wani yaro ya bar karatun Boko

Idan ba ku manta ba hakan ya zo ne bayan an hallaka wani babban Mawaki a Garin mai suna Osayamore Joseph. Jami’ar ta UNIBEN dai har yanzu ba tace ga abin da ya faru ba game da wannan babban rashi na Farfesa Otasowie.

Shugaban Jami’ar ya koka game da yadda sha’anin tsaro ya tabarbare a Garin sai dai Jami’an ‘Yan Sanda sun ce an kama wasu har mutane 3 da ake zargi da hannu da laifin kashe Farfesan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel