Kotu ta tasa ƙeyar wasu mutane biyu zuwa Kurkuku da suka ci miliyan 600 daga cikin kuɗin makamai

Kotu ta tasa ƙeyar wasu mutane biyu zuwa Kurkuku da suka ci miliyan 600 daga cikin kuɗin makamai

Hukumar yaki da cin hanci da yai ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta tasa keyar wasu mutane biyu dake hannu cikin bahallatsar kudin makamai gaban wata babbar kotun tarayya.

Jaridar Premium Times ta ruwaito, mutanen sun hada da Aliyu Usman da Nuru Usman, inda suka gurfana gaban alkali mai shari’a John Tsoho akan aikata laifuka da suka shafi satar kudi.

KU KARANTA: Sanata Kwankwaso yayi haɗuwar mamaki da wani ɗalibin daya taimaka yayin dayake gwamna (Hotuna)

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito an karanta ma mutanen biyu laifinsu kamar haka: “Aliyu Usman da Nura Usman manajan kamfanin Leaderette a ranar 10 ga watan Yuni an 2013 kun amshi naira miliyan 240 daga ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara akan tsaro.

Kotu ta tasa ƙeyar wasu mutane biyu zuwa Kurkuku da suka ci miliyan 600 daga cikin kuɗin makamai

Jami'an EFCC

“Kun amshi kudin na ta asusun banki mai lamba 1013621286 na bankin UBA, wanda ya kamata ku gane cewar kudi ne haramtattu”

Sai dai dukkanin mutanen biyu sun musanta zargin, inda bayan sauraron lauyoyi masu kara da na masu kariya, sai alkalin kotun mai shari’a John Tsoho ya bada belinsu akan kudi Naira miliyan 100.

Bugu da kari zasu kawo mutum daya kowannesu da zai tsaya musu, shima zai ajiye naira miliyan 100, tare da takardun kadararsa a babban birnin tarayya, Abuja.

Daga karshe mai shari’an ya dage sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Nuwamba, kuma ya aika da mutanen da ake zargi gidan yari har sai sun cika sharuddan beli.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Yaki da rashawa:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel