Ina son komawa Makarantar Boko Inji mai tallar gyada

Ina son komawa Makarantar Boko Inji mai tallar gyada

- Wani yaro da ke tallar gyada yace zai so ya koma karatun Boko

- Talauci ya sa Sunday Nwaeke ya bar zuwa Makaranta don dole

- A yanzu haka ya koma saidawa kanwar Mahaifiyar sa gyada

Wani mai tallar gyada yace yana sha'awar ya koma karatun Boko. Wannan yaro dan shekara 9 mai suna Sunday ya fara Makaranta a baya amma ya bari.

Ina son komawa Makarantar Boko Inji mai tallar gyada

Sunday ya bar karatu ya koma talla

Kowa ya san wannan yaro a Makarantar gaba da Sakandare ta Polytechnic din Oko da ke Anambra da mai gyada. Wannan yaro ya fara karatun Boko a baya inda har ya kai aji biyu (2) a Garin Ebonyi amma yanzu dole ta sa ya koma tallar gyada tare da wata 'Yar uwar Mahaifiyar sa.

KU KARANTA: An zargi wani Gwamna da shirin rusa PDP

A wata hira da yayi da wani mai suna Bennett Nwankwo ya bayyana cewa ba don talauci da yayi masu katutu ba da yanzu yana aji. Don haka ne wata Baiwar Allah Susie Retty ta ke cigiyar wannan yaro domin ceto sa daga wannan kangi. Mun samu wannan rahoto ne daga Gistreel.

Yanzu haka dai iyayen wannan yaro su na can Garin Ebonyi inda shi kuma yana Garin Anambra yana harkar saida gyada a Makaranta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel