Abdullahi Sugar ya goyi bayan Atiku da ya tsaya takarar shugabancin kasa a 2019

Abdullahi Sugar ya goyi bayan Atiku da ya tsaya takarar shugabancin kasa a 2019

- Alhaji Muhammadu Abdullahi Sugar yace Atiku Abubakar zai iya gyara Najeriya cikin kankanin lokaci idan aka bashi damar shugabanci

- Ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar zai yi amfani da sumfurin marigayi Shehu Musa Yar’adua wajen daidaita arzikin kasar

- Atiku ya karyata cewan ya fara yakin neman zabe don zaben 2019

Alhaji Muhammadu Abdullahi Sugar ya ce tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na da kwarewa da wayewar da ake bukata wajen magance matsalolin da kasar ke fuskanta.

Abudullahi Sugar, mukusancin Atiku, a wani hira da yayi da jaridar Daily Trust ya goyi bayan tsohon mataimakin shugaban kasar da ya karbi mulki daga hannun shugaba Muhammadu Buhari a 2019.

Yace Atiku na da tarin sani wajen gyara kasar cikin dan kankanin lokaci idan har aka bashi damar shugabanci.

Ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar zai yi amfani da sumfurin marigayi Shehu Musa Yar’adua wajen daidaita arzikin kasar.

KU KARANTA KUMA: An dakatar da shugaban NHIS Usman Yusuf har sai baba ya gani

A halin yanzu, Atiku Abubakar ya wanke zargin dake yawo game da rahotannin buhuhunan shinkafa dake dauke da sunansa da hotonsa akan shirin san a tsayawa takarar 2019.

Atiku wanda yayi magana ta shafin Facebook ya karyata cewar ya fara irin wannan yakin neman zabe.

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel