Yadda wata mata ta haihu a cikin mota yayin da take kan hanyar zuwa Legas

Yadda wata mata ta haihu a cikin mota yayin da take kan hanyar zuwa Legas

Hukumar kiyaye haddura ta kasa, FRSC a jihar Ogun ta sanar da sauka lafiya da wata mata tayi yayin da nakuda ya kamata a cikin mota, inda jami’an hukumar suka taimake ta wajen karbar haihuwar.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Alhamis 5 ga watan Oktoba, kamar yadda Kaakakin hukumar Florence Okpe ta bayyana, inda tace haihuwa ya kama matar ne yayin da take kan hanyar Ibadan zuwa Legas.

KU KARANTA: Sanata Kwankwaso yayi haɗuwar mamaki da wani ɗalibin daya taimaka yayin dayake gwamna (Hotuna)

“Da misalin karfe 1 na rana a ranar Laraba jami’an mu suka karbi haihuwar wata mata dake kan hanyarta ta zuwa Legas daga Ibadan a cikin motar haya mai lamba XF 365 MKD.

Yadda wata mata ta haihu a cikin mota yayin da take kan hanyar zuwa Legas

Ajoke

“Direban motar ya shiga ofishin mu na bada agajin gaggawa dake kan babban hanyar, inda ya bamu rahoton wata mata mai suna Ajoke Ahmad ta fara nakuda, sai muka fara shawarar garzayawa da ita Asibiti.

“Sai dai kafin mu wuce da ita zuwa Asibiti, nakudan yayi zafi har jaririn ya fara fitowa, daga nan ne sai jami’an mu suka taimake wajen karbar haihuwar. Kuma uwar da yaron suna cikin koshin lafiya.” Inji sanarwar.

Jami'an nan da duk mutanen da suka taimaka ma matar nan sun cancani yabo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Menene ra'ayin yan Najeriya game da mulkin Buhari?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel