An dakatar da shugaban NHIS Usman Yusuf har sai baba ya gani

An dakatar da shugaban NHIS Usman Yusuf har sai baba ya gani

- Ministan lafiya ya maida dakatarwan sakataren hukumar NHIS zuwa na sai baba ya gani

- Usman Yusuf na fuskantar dakatarwa na zuwa lokacin da za’a kammala bincike a zargin zamba da ake masa

- Kwamitin dake duba zuwa ga zargin sun kama shi da hannu dumu-dumu a cikin laifin

Ministan lafiya na Najeriya, Isaac Adewole ya sanar da dakatar da babban sakataren hukumar inshora na lafiya (NHIS), Usman Yusuf har sai baba illa-ma-shaa Allahu.

An dakatar da Mista Yusuf tun ranar 6 ga watan Yulin 2017, bayan an zarge shi da aikata zamba. Bisa ga umurni daga minister Adewole, domin gudanar da bincike mai inganci akan zargin da ake ma shugaban na NHIS.

A cewar Premium Times, bayan kammala bincike, a wani wasika zwa ga shugaban na NHIS wanda aka aika a ranar 5 ga watan Oktoba, Mista Adewale ya nuna cewa kwamitin sun gabatar da rahoton.

An dakatar da shugaban NHIS Usman Yusuf har sai baba ya gani

An dakatar da shugaban NHIS Usman Yusuf har sai baba ya gani

Ya kuma ce an tura rahoton ga shugaban kasa Muhmmadu Buhari. Mista Adewole yace kwamitin ta kama Mista Yusuf da hannu dumudumu a gurare da dama.

Dakatar da shi ya kawo cece-kuce da dama da majalisar wakilai inda suka bukaci a dawo dashi.

KU KARANTA KUMA: Dalibi ya kwankwadi madarar fiya-fiya domin nuna kin amincewar sa da faduwa jarrabawa

Mista Yusuf ma ya maida martani ga ministan cewa ba zai bi umurnin dakatarwan ba, cewa ministan baida ikon dakatar da shi.

Bayan Mista Yusuf, an dakatar da wasu manyan ma’aikata takwas a hukumar bisa zargin rashawa. Attahiru Ibrahim na aiki a matsayin mukaddashin sakatare.

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel