Gwamnatin Buhari ta baiwa ýan kwangila naira biliyan 100 na yin aiian manyan tituna 25 a Najeriya

Gwamnatin Buhari ta baiwa ýan kwangila naira biliyan 100 na yin aiian manyan tituna 25 a Najeriya

- Gwamnatin Najeriya ta samo naira biliyan 100 daga tsarin kasuwanci na Sukuk

- Gwamnati zata yi amfani da kudin ne wajen gina da gayaran hanyoyi 25 a fadin kasar nan

Ma’aikatar ayyukan, gidaje da lantarki ta samu naira biliyan 100 don yin manyan ayyukan hanyoyi da zasu taimaka ma yanayin kasuwanci a Najeriya, tare da inganta tattalin arziki.

A iya cewa wannan shine rance da gwamnatin Najeriya ta taba samu mafi sauki kuma cikin kankanin lokaci, inda aka samu kudaden bayan kwanaki 9 da mika takardar nemansu.

KU KARANTA: Rundunar Soji ta yi ma mayaƙan Boko Haram shigan ba zata, sun ranta a na kare

Jaridar The Cable ta bayyana wadannan makudan biliyoyi da gwamantin Najeriya ta samo su rance daga tsarin Sukuk, za’a biya su ne ba tare da kudin ruwa ba.

Gwamnatin Buhari ta baiwa ýan kwangila naira biliyan 100 na yin aiian manyan tituna 25 a Najeriya

Yayin bada cikin kudin

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito ministan kudi Kemi Adeosun ne ta mika ma ministan ayyukan Fashola cekin kudin, inda aka jiyo Fashola yana fadin “Wannan shine kudin Sukuk na farko da gwamnatin Najeriya ta fara samu, zamu yi amfani da kudaden wajen cigaba da manyan ayyukan da aka tsara a cikin kasafin kudin bana.

Gwamnatin Buhari ta baiwa ýan kwangila naira biliyan 100 na yin aiian manyan tituna 25 a Najeriya

Hanyoyin da za'ayi

“Ayyukan kuwa sune manyan hanyoyi guda 25, masu nasaba da habbaka tattalin arzikin kasa a dukkanin yankuna 6 na kasar nan, muna sa ran titunan zasu rage wahalar zirga zirga a fadin kasar nan

“An ware naira biliyan 16.67 da za’a kashe a kowane yankin kasar nan, inda akwai hanyoyi guda biyar-biyar a yankin Arewa ta tsakiya da Kudu maso kudu, yayin da Arewa maso gabas, Arewa ta yamma, da kudu maso gabas ke da hanyoyi hur-hudu. Sai kuma kudu maso yamma ke da manyan hanyoyi 3” Inji shi

Daga cikin hanyoyi da za’a fadada a Arewa sun hada da babban hanyar Kano zuwa Kaduna, Kano zuwa Maiduguri, Kano zuwa Katsina da kuma babbar hanyar kudancin Kano,sai kuma babban hanyar gabashin Kaduna.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel