Sanata Kwankwaso yayi haɗuwar mamaki da wani ɗalibin daya taimaka yayin dayake gwamna (Hotuna)

Sanata Kwankwaso yayi haɗuwar mamaki da wani ɗalibin daya taimaka yayin dayake gwamna (Hotuna)

- Wani direban jirgin sama da Kwankwaso ya taimaka ya tuka shi Abuja zuwa Legas

- Direban na daya daga cikin matasan da Kwankwaso ya kai karatu kasar waje

Alheri gadon barci, yadda ka shimfida shi, aka zaka kwanta akansa, haka zalika Hausawa na cewa abinda ka shua, shi zaka girba, in hairan hairan, in sharran sharran.

Tabbas alheri gadon barci, tunda tsohon gwamnan jihar Kano, kuma sanatan mai wakiltar Kano ta tsakiya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kwanta akan nasa yadda yayi shimfidar.

KU KARANTA; Rundunar Soji ta yi ma mayaƙan Boko Haram shigan ba zata, sun ranta a na kare

Me karatu a jiya Alhamis 5 ga watan Oktoba ne Sanata Rabiu Musa Kwankwaso akan hanyarsa ta zuwa jihar Legas daga babban tarayya Abuja, ya hau jirgin sama na wani kamfani mai zaman kansa, kamar yadda Umar Tanko Yakasai ma'abocin Facebook ya bayyana.

Sanata Kwankwaso yayi haɗuwar mamaki da wani ɗalibin daya taimaka yayin dayake gwamna (Hotuna)

Sanata Kwankwaso tare da Mahi

Sai dai cikin ikon Allah, ashe direban jirgin na daya daga cikin matasan da Sanata Kwankwaso ya tura su karatun koyon tukin jirgi kasar Jordan su 100, a zamanin dayake gwamnan jihar Kano karo na biyu, daga 2011-2017.

Sanata Kwankwaso yayi haɗuwar mamaki da wani ɗalibin daya taimaka yayin dayake gwamna (Hotuna)

Sanata Kwankwaso bayan isar sa Legas

Sai ga shi a shekaru 2 bayan barin sa mukamin gwamnan ya girbi abinda ya shuka, inda wannan matashi daya baiwa tallafin karatu, Mahi Sumaila ya zaman cikakken direban jirgin sama da kamfanin Azman, har ma su kayi hoto tare.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ganduje na aiki a jihar Kano, kalla a NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel