Wai yaushe Buhari zai tazo keyar barayin gwamnati zuwa gidan kaso - Lola Shoneyin

Wai yaushe Buhari zai tazo keyar barayin gwamnati zuwa gidan kaso - Lola Shoneyin

- Lola Shoneyin ta bayyana rashin jin dadinta ga shugaban kasar saboda har yazu ba a tura kowa kurkuku ba

- Misis Lola ta kasance daya daga wadanda ta yiwa shugaban kasa yakin neman zabe a zaben shekara ta 2015

- Lola ta ce tsarin da ake bi wajen nada mutane ofisoshi ya kasance mai ban mamaki kuma cike da rashin adalci

Fitaccen marubucin nan, Lola Shoneyin ta bayyana rashin jin dadinta ga shugaban kasar Muhammadu Buhari saboda har yanzu ba ta gan wanda aka tura a kurkuku ba, wanda ta sa ran cewa za a kama su kuma a tsare su don aikata laifin cin hanci a Najeriya da waje.

Yayin da take ganawa da SaharaTV, Misis Lola, wanda ta yiwa shugaban kasa yakin neman zabe a zaben shekara ta 2015 ta ce ta yi imanin cewa shugaba Buhari zai canza kasar, amma shugaban na kewaye da mutanen da ba su da gaskiya kuma basu da halayyar kirki.

Ta bayyana wannan saboda tsarin da ake bi wajen nada mutane zuwa ofisoshi ya kasance mai ban mamaki kuma cike da rashin adalci.

Wai yaushe Buhari zai tazo keyar barayin gwamnati zuwa gidan kaso - Lola Shoneyin

Shugaban kasar, Muhammadu Buhari

KU KARANTA: Gwamnatin Sakkwato ta yi Allah wadai da EFCC a kan zargin Tambuwal

"Har ila yau, ta ci gaba da cewa, ta zabi daya daga cikin manyan ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2015, wanda ta kawo shugaba Buhari ga mulki”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel