Dalilin da yasa EFCC ke neman gurfanar da ni gaban shari'a - Patience Jonathan

Dalilin da yasa EFCC ke neman gurfanar da ni gaban shari'a - Patience Jonathan

- Matar tsohon shugaban kasa wato Patience Jonathan ta bayyana dalilin da yasa EFFC ke kokarin gurfanar da ita gaban shari'a

- A bayanin nata, ta shafawa tsohon shugaban hukumar ta EFCC, Ibrhahim Larmode, bakin fenti

- Ta ce zargin da ake mata ya danganci zaben da ya gabata ne a 2015

Matar tsohon shugaban kasa wato Patience Jonathan ta ce binciken da EFCC ke gudanarwa a kan ta ya danganci bayyana ra'ayoyin ta da ta yi ne game da Buhari yayin kamfen din zaben 2015.

Ta fadi hakan ne a ranar Alhamis 5 ga wannan wata. Naij.com ta kawo maku cewan Patience Jonathan ta zargi hukumar da keta huruminta da na makarraban ta. Ta yi wannan zargi ne a wani kara da ta shigar a wani babban kotu a Abuja.

Dalilin da yasa EFCC ke neman gurfanar da ni gaban shari'a - Patience Jonathan

Dalilin da yasa EFCC ke neman gurfanar da ni gaban shari'a - Patience Jonathan

A wata takardar kara da lauyanta ya gabatar, ta yi bayanin yadda tsohon shugaban EFCC wato Ibrahim Larmode ya bata shawaran bude wasu asusun banki guda biyar a bankin skye wanda a halin yanzun EFCC ta dakatar da asusun.

DUBA WANNAN: Makarfi yayi magana a kan takarar shugabancin kasar Fayose

Ta ce ya bata shawaran bude su ne don ta samu tafiyar da makudan kudi don neman magani a turai ba tare da ta karya wata doka da ke gwame da tafiyar da kudade ba.

Idan mai karatu bai manta ba Naij.com ta kawo maku yadda majalisar dattawa ta yi barazanar samar da takardar izinin kama shugaban rikon kwarya na hukumar ta EFCC wato Ibrahim magu, sakamakon karar sa da Patience.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel