Shugaba Buhari ya nada Aisha Ahmad a matsayin mataimakiyar gwamnan bankin kasa: Ko kunsan wacece ita?

Shugaba Buhari ya nada Aisha Ahmad a matsayin mataimakiyar gwamnan bankin kasa: Ko kunsan wacece ita?

- Tana da digiri har uku duk a harkar sarrafa kudi

- Tana da aure da ’ya’ya biyu

- Ta rike manyan mukamai bankunan a Stanbic IBTC da kuma Diamond Bank

Aisha Ahmad, ’yar shekara 40, hamshakiyar ma’aikaciyar banki ce tun kusan shekaru 20. Ta rike mukamai da dama a harkar banki wanda suka hada da kula da hannayen jari, kula da tattalin arziki, mai bada shawara a kan yadda ya kamata a yi amfani da kudi, da sauran su.

Shugaba Buhari ya nada Aisha Ahmad a matsayin mataimakiyar gwamnan bankin kasa: Ko kunsan wacece ita?

Aisha Ahmad

An haifi Aisha a ranar 26 ga watan Oktoba, a shekara ta 1977, a jihar Neja. Ta karanci Accounting a digirinta na farko a jami’ar Abuja. Sannan tayi digirin kwarewa (masters) a Business Administration and Finance daga jami’ar Legas. Daga baya kuma ta kara sabon digirin kwarewa a Finance & Management daga jam’iar Cranfield dake Birtaniya. Ta auri tsohon brigediya-janar Abdallah Ahmad kuma suna da ’ya’ya biyu maza.

DUBA WANNAN: Ballewar annobar kyandar biri: Yadda zaku kare kan ku daga kamuwa da kwayar cutar

Kafin a bata mukamin maitamakiyar shugaban babban bankin Najeriya (CBN), ita ce shugabar bankin Diamond Bank Plc., kuma ita ce shugabar majalisar mata shuwagabanni a ma’aikatu da gwamnati (Women in Management, Business and Public Service). An kafa majalisar ne a 2001 don hada kan mata shuwagabanni da kuma bunkasa yadda zasu tafi da ma’aikatar da suke shugabanta.

Aisha tayi aiki da NAL Bank Plc., Zenith Bank Plc., da kuma Stanbic IBTC Bank kafin ta zama shugaba a Stanbic din. Tana cikin kungiyoyin Chartered Financial Analyst, CFA, da Chartered Alternative Investment Analyst, CIAI.

Aisha ta gaji kujerar, Sarah Alade, ce bayan da tayi ritaya a watan Maris na bana. Ita Sarah ita ce mace ta farko data fara rike babban mukami a babban bankin Najeriya.

An sanar da nada ta a wannan mukami daga ofishin shugaban kasa a yau, kuma zata shiga ofis din mataimakin gwamnan CBN da zarar majalisar dattijai ta rantsar da ita.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel