Gwamnatin Sakkwato ta yi Allah wadai da EFCC a kan zargin Tambuwal

Gwamnatin Sakkwato ta yi Allah wadai da EFCC a kan zargin Tambuwal

- Jami'ai gwamnatin jihar Sakkwato sun zargi EFCC game da ƙoƙarin lalata amincin gwamna Aminu Waziri Tambuwal

- Hukumar EFCC ta kalubalanci ikon gwamnan Tambuwal a kan yafe wasu mutane 5 da ake tuhuma don aikata laifukan cin hanci

- Tsohon gwamna Attahiru Bafarawa ya kasance daga cikin wadanda ake tuhuma a shari'ar

Jami'ai gwamnatin jihar Sakkwato sun zargi hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) game da ƙoƙari na lalata amincin gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

NAIJ.com ta tattaro cewa, a makon da ta gabata ne hukumar ta kalubalanci ikon gwamnan Tambuwal da ya yafe wasu mutane 5 da ake tuhuma don aikata laifukan cin hanci da rashawa wanda suka aikata a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar, Attahiru Bafarawa wanda ya yi mulki tsakanin 1999 zuwa 2007.

Wadanda ake tuhuma sun hada da kwamishinoni na yanzu guda 2, Tukur Alkali da Isa Achida. Sauran su ne shugaban NCCE, Alhaji Maigari Dingyadi da dan majalisar dokoki mai wakiltar mazabar Isa, Alhaji Habibu Modachi da kuma sakatare na din din din, Isah Bello.

Gwamnatin Sakkwato ta yi Allah wadai da EFCC a kan zargin Tambuwal

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal

An gurfanar da su a shekara ta 2009, shekaru biyu bayan gwamnatin Bafarawa, bisa zargin cin hanci da rashawa na naira biliyan 15.

KU KARANTA: CBN ta karyata kamun mataimakin gwamnan ta

Tsohon gwamnan ya kasance daga cikin wadanda ake tuhuma a shari'ar.

Da yake bayani, babban jami'in gwamnati a ma'aikatar shari'a ta jihar ya ce EFCC na da gaskiya a kan batun.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel